Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kawo ƙarshen rikicin gonaki da ya shafe shekaru 47 yana ci gaba tsakanin al’ummar Jobi da ke ƙaramar Hukumar Maigatari a Jihar Jigawa da kuma al’ummar Kyalli da ke Jamhuriyar Nijar, bayan ƙaddamar da rabon madadin gonaki ga manoman da rikicin ya shafa.
Matakin ya biyo bayan aiwatar da shawarwarin da Kwamitin Iyakokin Jihar Jigawa da kuma Hukumar Kula da Iyakokin ƙasa ta Nijeriya (NBC) suka bayar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jigawa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce, an gudanar da bikin rabon gonakin ne a Dajin Dan-Makama, wanda hakan ya kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana kawo cikas ga zaman lafiya tsakanin al’ummomin biyu da ke makwabtaka da juna a kan iyakar ƙasashen Nijeriya da Nijar.
Da yake jawabi, Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan rana ta kasance abin tarihi.
“Alhamdulillah. Yau rana ce ta tarihi, domin Allah Ya haɗa mu domin kawo ƙarshen rashin fahimtar juna da ya daɗe tsakanin al’ummar Jobi da ke Maigatari a Jihar Jigawa da kuma al’ummar Kyalli ta Jamhuriyar Nijar,” inji gwamnan.
Ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan manoman Jobi, waɗanda suka shafe shekaru suna noma a ƙasar Kyalli, suka rasa damar ci gaba da noma a wurin sakamakon fara aiwatar da dokokin da suka shafi iyakokin ƙasashen duniya.
Gwamnan ya yaba wa Hukumar Kula da Iyakokin ƙasa ta Nijeriya (NBC) bisa rawar da ta taka wajen sasanta rikicin, yana mai cewa ci gaba da tattaunawa da bayar da shawarwari daga hukumar ne suka taimaka wajen cimma wannan sulhu cikin lumana.
Haka zalika, ya jinjinawa Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Injiniya Aminu Usman, mambobin Kwamitin Iyakokin Jihar, sarakunan gargajiya, shugabannin ƙananan hukumomi, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki saboda gudunmawar da suka bayar wajen warware rikicin.
Namadi ya kuma yaba wa al’ummar Jobi bisa yadda suka amince da barin gonakin da suka shafe shekaru suna noma domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
“Babbar godiyarmu ta musamman ta tabbata ga mutanen Jobi. Ba abu ne mai sauƙi mutum ya bar gonakin da ya saba noma tsawon shekaru ba, amma sun karɓi wannan mataki cikin haƙuri, fahimta da kuma sadaukarwa domin zaman lafiya,” inji shi.
Tun da farko, Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa kuma Shugaban Kwamitin Iyakokin Jihar, Injiniya Aminu Usman, ya ce kwamitin ya ba da shawarar cewa manoman Jobi su daina noma a ƙasar da ke cikin yankin Kyalli na Jamhuriyar Nijar, yayin da gwamnatin jihar za ta samar musu da madadin gonaki a cikin Jigawa.
Ya bayyana cewa bayan amincewar gwamna, an ware wani ɓangare na Dajin Dan-Makama domin aikin noma, inda manoma 74 da rikicin ya shafa suka samu sabbin gonaki.
A saƙon fatan alheri da ta gabatar a madadin Babban Daraktan Hukumar Kula da Iyakokin ƙasa ta Nijeriya (NBC), Surɓ. Adamu Adaji, Hajiya Yahanasu Aliyu ta yaba wa Gwamna Namadi bisa karɓar shawarar hukumar na samar wa manoman da abin ya shafa sabbin gonaki.
Ta bayyana matakin a matsayin abin koyi na shugabanci nagari da kuma jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankunan da ke kan iyaka.
Rahoton ya nuna cewa Nijeriya da Jamhuriyar Nijar na da doguwar iyaka da ta ratsa jihohi da dama na Arewacin Nijeriya. Duk da kyakkyawar alaƙar tarihi, al’adu da kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu, rikice-rikicen da suka shafi iyaka kan taɓa shafar manoma da makiyaya, lamarin da ya sa warware irin waɗannan matsaloli cikin lumana ke da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.
