
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, ya nuna amincewa da goyon bayansa akan gyare-gyaren al’amuran tattalin arziƙi da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samar, inda ya yaba wa Babban Bankin Nijeriya (CBN) bisa ɗaukar matakan dawo da ɗorewa al’amura a ƙasar.
Sarkin, wanda tsohon gwamnan CBN ne, ya ce ƙasar ta farfaɗo daga halin taɓarɓarewar lamuran tattalin arziƙi sakamakon warware matsalolin samar da wadatar kuɗi, rage matsin hauhawar farashi da ɗorewar matakin canjin kuɗi.
Mai Martaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabin akan fannin tattali, inda ya ce ba shi da wani abu da zai ce face ya yaba wa CBN bisa ƙoƙarin da ya yi na taimaka wa matakan gyaran harkar tattalin da shugaban ƙasar ya ɗauko.
A cewarsa, Nijeriya ta farfaɗo daga halin matsi tattalin arziƙi da ta tsinci kanta a ciki a baya sakamakon rashin samu daidaito a al’amuran kuɗaɗe da rashin samar da wadatar raba kuɗaɗe, yana mai cewa CBN ya shafe tsawon shekara guda yana ƙoƙarin aiwatar da matakan da za su taimaka wa samun wadatar kuɗi.
Ya bayyana cewa, duk da cewa matakin riba (interest) na da yawa, gyare-gyaren suna taimaka wa ɗorewar darajar naira da inganta tattalin arziƙin ƙasar, wanda ya sa matakin faɗuwarta ya ragu daga shekara ɗaya zuwa yanzu.
Haka kuma, ya ce Nijeriya ta yi nasarar samar da sama da Dala biliyan 40 a asusunta na ajiyar rarar kuɗaɗe a ƙasashen waje sakamakon matakan shugaban, yana mai bayyana hakan a matsayin gagarumar nasara.
