Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya shirya ware kashi 33 cikin 100 na dukiyarsa domin ayyukan jinƙai a matsayin wani ɓangare na tsarin gadon dukiyarsa, kamar yadda ‘yarsa, Halima Dangote, ta bayyana.
Halima, wadda ke cikin amintattun membobin Gidauniyar Aliko Dangote, ta bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin Bloomberg ya wallafa ranar Talata.
Ta ce, Dangote ya samu amincewar iyalansa na ware kaso ɗaya bisa uku na dukiyarsa domin tallafa wa ayyukan jinƙai da ci gaban al’umma.
Bisa ƙididdigar Bloomberg Billionaires Indeɗ, dukiyar Dangote ta kai kimanin dala biliyan 35.1. Idan aka ware kashi 33 cikin 100 na wannan dukiya, hakan zai kai kusan dala biliyan 11.7 da za a miƙa ga ayyukan alheri.
Halima ta bayyana cewa mahaifinta yana kallon ayyukan jin kai a matsayin muhimmin ginshiƙi na abin da zai bari a baya, saboda haka ya haɗa wannan tsari cikin shirinsa na rabon gado.
Ta ce, “Mahaifina ya tsara komai ta yadda gidauniyar za ta fi mayar da hankali kan inganta harkokin lafiya da ilimi. Ya kuma ba gidauniyar kaso mai yawa na dukiyarsa. A tsarin Shari’ar Musulunci, ya ware kashi 33 cikin 100 na dukiyar gadonsa domin ayyukan alheri.”
A cewarta, manufar hakan ita ce tabbatar da cewa ayyukan jin kai za su ci gaba har zuwa tsararraki masu zuwa.
Halima ta ƙara da cewa, bayar da gudunmawa ga al’umma wani muhimmin ɓangare ne na rayuwar iyalinsu, domin sun yi imanin cewa nasarar kasuwancinsu ta samo asali ne tare da taimakon al’umma.
Ta bayyana cewa, Dangote ya bukaci ita da ‘yan uwanta mata biyu tare da mahaifiyarsa su sanya hannu a takardar wasiyyar da ta ba shi damar ware wannan kaso na dukiyarsa domin amfanin bil’adama.
Wannan sabon shiri ya ƙara ƙarfafa ayyukan jin kai da Dangote ya fara tun shekarar 1994 lokacin da ya kafa Gidauniyar Aliko Dangote.
A cewar Halima, gidauniyar ta samu asusun farko na dala biliyan 1.25 kimanin shekara goma da suka gabata, sannan daga baya aka ƙara mata dala miliyan 700 domin faɗaɗa ayyukanta.
Ta ce kusan kashi 70 cikin 100 na kuɗaɗen da gidauniyar ke kashewa na zuwa ne ga ayyukan ci gaba a Nijeriya, yayin da kashi 20 cikin 100 ke tallafa wa shirye-shirye a sauran ƙasashen Afirka. Sauran kuɗaɗen kuma ana kashe su ne a wasu ƙasashe na duniya.
Ayyukan gidauniyar sun haɗa da tallafa wa harkokin lafiya, ilimi, inganta abinci da ayyukan agaji. Haka kuma ta yi haɗin gwiwa da Gidauniyar Bill & Melinda Gates da gwamnatocin jihohin Arewacin Nijeriya wajen yaƙi da cutar shan inna, wanda ya taimaka wajen kawar da cutar a nahiyar Afirka.
Matakin da Dangote ya ɗauka ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara mayar da hankali a duniya kan yadda attajirai ke amfani da dukiyoyinsu wajen ayyukan jinƙai. Duk da cewa kaso 33 cikin 100 bai kai rabin dukiyar da wasu attajiran duniya ke bayarwa ba, ana kallon wannan a matsayin ɗaya daga cikin manyan alkawurran bayar da gudunmawar jin kai da wani attajirin Afirka ya taɓa yi.
A farkon wannan shekara, mujallar TIME ta saka Aliko Dangote cikin jerin fitattun masu ayyukan jinƙai a duniya na TIME100 Philanthropy, inda ta yaba wa irin gudunmawar da Gidauniyar Aliko Dangote ke bayarwa, wadda ake kiyasin tana kashe sama da naira biliyan 50 a duk shekara wajen ayyukan ci gaba a sassa daban-daban na Afirka.
