Yadda tallace-tallacen damfara da AI ke cin gajiyar tsarin talla na TikTok wajen yaudarar ’yan Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Yayin da TikTok ke ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan kafafen sada zumunta da ‘yan Nijeriya ke amfani da su, wasu masu damfara sun fara amfani da ƙirƙirarriyar fasahar ta AI wajen ƙirƙirar tallace-tallacen bogi da ke kwaikwayon manyan kamfanoni da fitattun mutane domin yaudarar jama’a.

Wannan bincike na musamman ya bankaɗo yadda ake amfani da tsarin tallan TikTok wajen yaudarar masu amfani da shi, tare da jefa dubban mutane cikin asarar kuɗi da satar bayanansu na sirri.

Lokacin da Mohammed Yusuf ya yi murabus daga aikinsa na malanta a Ilorin, Jihar Kwara, a watan Oktoban 2025 saboda ƙarancin albashi, ya yi fatan samun wata hanyar samun kuɗin shiga da za ta taimaka masa ya tsallake matsin tattalin arzikin Nijeriya.

Bayan makonni yana neman aiki ba tare da nasara ba, ya karɓi bashi domin fara kasuwancin PoS, yana mai fatan hakan zai zama mafita gare shi.

Yayin da yake binciken hanyoyin samun kuɗi ta yanar gizo, tsarin TikTok ya fara nuna masa jerin tallace-tallacen bidiyo da ke alƙawarin bayar da tallafi, rance, kyaututtuka da damar saka hannun jari.

ɗaya daga cikin tallace-tallacen, wanda ke ɗauke da tambarin OPay da kuma muryar da ta yi kama da ta ɗan Nijeriya, ya yi iƙirarin cewa kamfanin yana rabon na’urorin PoS kyauta tare da tallafin kuɗi har Naira 200,000 ga masu gudanar da kasuwancin PoS.

Da ya amince da tayin, Yusuf ya danna hanyar haɗin da aka bayar, inda ya cike lambar wayarsa da bayanan asusun OPay ɗinsa, ba tare da sanin cewa tallar ta amfani da AI aka ƙirƙira domin damfarar jama’a ba.

Bayan wasu sa’o’i, wani mutum da ya gabatar da kansa a matsayin jami’in OPay ya kira shi, ya tattauna yadda za a kai masa na’urar PoS, sannan ya nemi lambar tabbatar da mu’amala ta OTP da sunan tabbatar da cancantarsa.

“Na ga bidiyon wani ma’aikacin OPay ne a TikTok yana cewa za su ba mu kuɗi da PoS. Har ma an nuna tallar a matsayin talla da aka biya kuɗi. Ban taɓa zargin damfara ba ne,” inji shi.

Sai dai da ya koma wajen kasuwancinsa daga baya, ya gano cewa kusan Naira 150,000, kusan dukkan jarin da ya fara da shi, an kwashe ta ta hanyar sayen tikitin caca na SportyBet ba tare da izininsa ba.

“Na yi kuka sosai ranar. Kuɗin aro ne na fara kasuwancin. Har yanzu ina tuna lokacin da na kira mutumin, ya ɗaga waya ya ce min kawai, ‘Na damfare ka’,” inji Yusuf.

Da ya kai ƙorafi ga OPay, an sanar da shi cewa kuɗin sun fita ne ta mu’amaloli daban-daban zuwa SportyBet, amma ba za su iya dawo da su ba.

Bincike ya gano cewa lamarin Yusuf ba shi kaɗai ba ne.

An gano cewa ana amfani da bidiyoyin AI, deepfake da kwaikwayon murya wajen ƙirƙirar tallace-tallacen bogi da ke amfani da sunayen manyan kamfanoni da fitattun mutane domin yaudarar masu amfani da TikTok.

Wazannan tallace-tallace na kwaikwayon kamfanoni irin su:

OPay, United Bank for Africa (UBA), MTN, Airtel.

Haka kuma ana amfani da hotuna da bidiyon fitattun mutane kamar:

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, Alhaji Aliko Dangote, Shugaban UBA, Tony Elumelu.

An sarrafa bidiyoyinsu da AI domin su bayyana kamar suna tallata shirye-shiryen bogi.

Duk da cewa dokokin TikTok sun haramta damfara, kwaikwayon mutane da yaudarar jama’a, binciken ya nuna cewa waɗannan tallace-tallace na ci gaba da bayyana a matsayin tallace-tallacen da aka biya kuɗi, wato Sponsored Ads.

Masana harkokin tsaro ta yanar gizo sun bayyana cewa masu damfara suna cin gajiyar amincewar da jama’a ke yi wa TikTok.

Sun ce idan mutum ya ga talla da aka biya kuɗi, yawanci yana ɗauka cewa kamfanin ya tantance ta kafin ya amince da ita.

Wani matashi, Ahmad Wura, ya ce ya tara kadarorin kuɗaɗen intanet (cryptocurrency) da suka kai kusan Naira miliyan ɗaya bayan watanni yana ciniki.

Sai dai wata talla da ya gani a TikTok ta yi masa alƙawarin ninka kuɗinsa ta hanyar wani shirin horo kan cinikin crypto.

Bayan ya cike bayanansa, masu damfarar sun kutsa cikin asusun imel ɗinsa tare da mallakar wallet ɗinsa na Bybit, inda suka kwashe duk kadarorinsa.

“Na shiga tashin hankali sosai. Sun karɓe min imel, Google Authenticator da komai,” inji shi.

Tsakanin Afrilu zuwa Mayun 2026, wannan bincike ya bibiyi tallace-tallace 130 da ake zargin na damfara ne.

An gano cewa: OPay ce aka fi amfani da sunanta.

Ana kuma amfani da sunayen gwamnoni irin su Babajide Sanwo-Olu, Seyi Makinde da Ademola Adeleke.

Tallace-tallacen suna zuwa cikin Turanci, Hausa, Yarbanci da Pidgin.

Yawancinsu ba sa nuna alamar cewa AI ce ta ƙirƙire su, duk da cewa dokokin TikTok sun wajabta hakan.

Masana sun ce masu damfarar na amfani da kalmomi irin su: “Ka nema yanzu.” “Dama ta ƙarshe.” “Gurbi kaɗan suka rage.” Domin matsa wa mutane su ɗauki mataki cikin gaggawa.

Masanin tsaro ta yanar gizo, Michael Ukachi, ya ce masu damfara sun fahimci yadda mutane ke yarda da tallace-tallacen da aka biya kuɗi.

A cewarsa: “Yanzu AI ta sauƙaƙa ƙirƙirar bidiyoyin bogi masu kama da na gaske. Abin da da sai gungun mutane sun yi, mutum guda na iya yi cikin ɗan lokaci.”

Shi ma lauya kuma masanin fasahar zamani, Damilare Adenola, ya ce bayanan da masu damfara ke tattarawa ba sa tsaya ga damfara guda ɗaya.

Ya ce ana iya amfani da su wajen satar bayanan mutum, kutse cikin asusu da kuma sauran laifukan yanar gizo.

Da aka tuntuɓi TikTok, Shugabar Sadarwa ta Kamfanin a yankin Afirka ta Kudu da Sahara, Keagile Makgoba, ta ce an cire tallace-tallacen da aka nuna musu.

Ta ce kamfanin na haramta duk wani talla mai yaudara kuma yana ɗaukar mataki idan an gano saɓawa.

Sai dai binciken ya nuna cewa duk da cire wasu, har yanzu ana ci gaba da samun irin waɗannan tallace-tallace a dandalin.

Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA) ta bayyana cewa dole ne kafafen sada zumunta su ƙara tsaurara matakan tantance masu talla.

Hukumar ta ce, wajibi ne a tabbatar cewa kamfanoni na gaskiya kaɗai ake bari su yi talla, tare da gano duk wani yunƙurin damfara kafin ya kai ga masu amfani.

By ukarofi