ICPC ta maka na hannun daman El-Rufa’i, Jimi Lawal da tsohon akanta janar a kotu

Daga BELLO A. BABAJI

An maka Jimi Lawal, wanda mai bai wa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i shawara ne a kotu, bisa laifin cin mutuncin aiki da badaƙalar wasu kuɗaɗe.

Hukumar Hana Rashawa da Laifuka ire-iren ta (ICPC), ta zarge shi ne da hannu a karɓar miliyan N64.8 daga asusun Gwamnatin jihar don biyan kamfanin Solar Life Nigeria Limited.

Za a gurfanar da shi ne tare da tsohon Kwamishinan Kuɗi na jihar, Yusuf Inuwa da tsohon Akanta-Janar, Umar Waziri da kuma kamfanin Solar Life Nigeria Limited.

ICPC ta ce babu wani aikin kwangila da Solar Life Nigeria Limited ya gudanar a jihar.

An biya Lawal wasu daga cikin kuɗaɗen ne daga asusun kuɗaɗen shiga (IGR) na jihar.

Za a gurfanar da tsofaffin jami’an ne a Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kaduna bayan shigar da ƙara akan su a ranar 15 ga watan Junairu da ICPC ta yi.

Kawo yanzu ba a sanya ranar da za a gudanar da sauraron ƙarar ba game da tuhumar tsofaffin manyan jami’an gwamnatin, kamar yadda ‘The Nation’ ta wallafa.