Idon Mikiya: Ba mu muka kar zomon ba – kamfanin Vision ya mayar wa Hukumar NBC martani

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Kamfanin Gidan Rediyon Vision FM da Gidan Talabijin na Farin Wata ya mayar da martani kan dakatar da shirinsa na ‘Idon Mikiya’ da Gwamnati Shugaba Buhari ta yi kan tattauna batun tsawaita naɗin da aka yi wa Daraktan Hukumar Leqen Asiri ta Ƙasa (NIA), Rufa’i Abubakar, da kuma zargin rashin iya aikinsa, kamfanin yana mai cewa, shine ya kar zomon ba, rataya aka ba shi.

Martanin da ya ke rubuce ne a wata takarda da Shugaban Kamfanin Yaɗa Labarai na Vision Media, Alhaji Umar Faruk Musa, ya aike wa Hukumar NBC, ya nuna cewa, batun da ake yin cece-kucen akan sa, ba shirin Idon Mikiya ne ya faro shi ba, domin kuwa kafafen yaɗa labarai da dama a Nijeriya ne suka yi ta dukan levva akai, inda har hankalin shirin na Idon Mikiya ya kai kai, saboda yadda ’yan Nijeriya suka damu da batun.

Alhaji Faruk ya ce, “mun rubuto wannan ne, domin alamta karɓar wasiƙarku mai kwanan wata 28 ga Janairu, 2022, da ke da lamba NBC/DGABV/LIC02/22 da kuma kira ga mutuntawa, don sake duba umarnin dakatar da shirinmu mai suna ‘IDON MIKIYA’ a tashar rediyon Vision FM da Tashar Talabijin ta Farin Wata, don adalci ga al’ummar Nijeriya gabaɗaya saboda dalilai kamar haka:

“Tattaunawarmu kan naɗi a Hukumar NIA ba ta ci karo da Sashe na 39(3) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ta ko’ina. A fahimtarmu, Sashe na 39(3) ya na magana ne kan batun daƙile masu riƙe da muƙaman gwamnati wajen bayyana ra’ayinsu a kafafen yaɗa labarai da ma sauran ’yan qasa bakiɗaya. Don haka bai kamata wannan ya janyo dakatarwa ba. Tattaunarwar da aka yi a shirin ba ta kai ga matakin bayyana wani sirrin ƙasa ko abinda ya shafi tsaron ƙasa ba, kuma bai dace a kalli lamarin a matsayin hakan ba.

“Haka nan, tattaunawa kan batun cancanta ka naɗin da aka yi a Hukumar NIA ta riga ta mamaye manyan kafafen sadarwa da na zamani tun gabanin ranar 5 ga Janairu, 2022. Shirin Idon Mikiya na ranar 5 ga Janairu, 2022, ba shi ne ya fara tsuro da batun naɗin da aka yi a NIA ba. Don haka idan adalci a ke son yi, to kamata ya yi a fara lalubo waɗanda suka fara tsuro da batun, a yi musu hukunci, idan ma har a na kallon batun a matsayin laifi kenan.

“Umarnin dakatar da shirin ya yi karo da adalci na gaskiya guda biyu. Dakatarwar ba ta nuna a ainihin guraren da aka aikata laifin ba a cikin shirin, waye ya furta laifin a masu gabatarwar, wacce hujja ce ta tabbatar da iƙirarin, waye ya ke da shaidar wuce gona da kuma dangantakar hakan da Sashe na 39(3) da ake zargin an saɓawa kafin a kai ga yanke hukuncin dakatar da shirin.”

Daga nan sai kamfanin na Vision Media ya ƙara da cewa, “ba a bi ƙa’idojin amsar koke ba, wanda Dokar Hukumar NBC a sassa na 14.3.1-14.3.6 da sashe na 12 na Dokar NBC ba. Kuma hukumar ta gaza wajen bin tsarin amsar ƙorafi tare da bayar da sanarwa kafin a bayar da umarnin dakatar da shirin.”

Ya cigaba da kira da cewa, “Idon Mikiya shiri ne da ya ke da masu sauraro da yawa a faɗin ƙasar. Ya na ilimintarwa kan bayanai da suka shafi ƙasa nan take. Dakatar da shirin ba cutarwa ne kaɗai ga mafi yawan ’yan Nijeriya ba, zai kuma jefa mafi yawansu a cikin duhun jahilci.”

Daga nan sai wasiƙar ta ƙara jan hankalin NBS da cewa, idan za ta iya tunawa, a dukkan ganawar da aka yi a baya tsakanin Hukumar da Kamfanin ba a taɓa samun kamfanin kafafen yaɗa labaran da karya doka a cikin shirin Idon Mikiya ba, inda ma sai tabbatar da cewa, shirin yana ƙoƙarin yin adalci yayin gabatar da shi, kuma masu gabatarwar ba sa nuna halin rashin adalci ga wani ɓangare.

Ya ƙara da cewa, a cikin shirin ranar 5 ga Janairu, 2022, an aikata adalci da daidaito, domin har ra’ayin Farfesa Sylvester Afolabi, wanda ya ke goyon bayan NIA, aka kawo, wanda kuma ya rubuta nasa sharhin ne a ranar 28 ga Disamba, 2021, gabanin shirin na Idon Mikiya.

Daga nan sai kafar yaɗa labaran Vision Media ta ƙara da cewa, “tun sa aka fara shirin Idon Mikiya fiye da shekaru goma da suka gabata, ba a taɓa samun shirin da laifin karya wata doka ba. Don haka sai kamfanin ya nemi da a janye hukuncin da Hukumar NBC ta yanke masa nan take na dakatarwa tsawon watanni shida da kuma tarar Naira Miliyan Biyar, yana mai kare ƙoƙarin masu gabatar da shirin wajen tabbatar da adalci a kowane lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *