Imam Suleiman ya shawarci matasa su ƙaurace wa ’yan siyasar sara-suka

Manhaja logo

Daga DAUDA USMAN a Legas 

Babban limamin masallacin Juma’a na rukunin gidajen unguwar Wantauzan a Victoria Ireland dake cikin birnin Legas, Sheikh Imam Suleman Ibrahim kuma shugaban ƙungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa Iƙamatussunah ta ƙasa reshen  jihar Legas ya ce ganin cewar lokacin siyasa yana ci gaba da ƙara tunkarowa, kuma mafi yawan ‘yan siyasa da sauran waɗansu al’ummar Musulmi sun sauka bisa kan sunnar Manzon Allah suna amfani da wannan lokacin suna ɓata yaran mutane a wajen koya masu shaye-shayen kayan maye tare da koya masu aikata miyagun ayyukan kaba’ira  domin biyan buƙatar kansu a wajen gudanar da harkokin siyasar ƙasar nan.

Ya ce hakan ba daidai ba ne, ya kamata su daina a maimakon hakan su cigaba da koya wa yaran tarbiyya tagari tare da ɗaukar nauyin su a wajen koya masu sana’o’n dogaro da kai domin cigaba da samun zaman lafiya da sauran makamantansu.

Imam Suleman Ibrahim wanda ya furta hakan a unguwar mile12 dake cikin garin Legas a lokacin da yake kan mumbarin wa’azi wanda ƙungiyar ta Izala a Legas ta shirya kuma take zagayawa duk bayan sati biyu domin faɗakar da al’umma a bisa kan mahimmancin zaman lafiya da haɗin kan al’ummar musulmin jihar Legas baki ɗaya.

Ya ce wajibi ne a wajen ɗan ƙasa nagari a cewar sa musamman ‘yan siyasa da shugabannin ta gaba ɗaya su cigaba da bai wa ƙasa gudunmawar su ta kawo wa al’ummar ƙasa zaman lafiya tare da haɗin kawunan junan su baki ɗaya.

Haka zalika ya cigaba da cewa akan haka yake ƙara shawartar ‘yan siyasar ƙasar nan da shuwagabannin ta da sauran shugabannin al’umma da su ƙara ƙoƙari wajen kawo abubuwan da za su ci gaba da zaunar da ƙasar nan lafiya tare da kawo cigaban al’ummar cikinta baki ɗaya.