Saboda girman hatsarin da ke tattare da zalunci da muninsa har Allah Ta’ala Ya hana taimakekeniya da Azzalumai da kuma karkata zuwa gare su.
“Kuma kada ku karkata zuwa ga azzalumai har wuta ta shafe ku kuma ba ku da wasu Majibinta bacin Allah, sannan ba za a taimake ku ba.”
Wannan ita ce ladabtarwar Alkur’ani kuma ladabtarwar Ahlul-Bait (A.S.), ruwayoyi da dama da suka zo daga gare su game da hana karkata zuwa ga azzulumai, da sadarwa da su, da yin haraka tare da su a cikin kowane irin aiki da taimakekeniya da su ko da kuwa daidai da kwatankwacin tsagin dibino.
Babu shakka mafi girman abinda aka yi hani a kansa a musulunci da kuma ga Musulmi shi ne sassauci ga azzalumai da rufe ido game da miyagun ayyukansa, da mu’amala da su, ballantana ma cuɗanya da su da taimaka musu da taimaka musu a kan zaluncinsa.
Babu abinda ya jawo wa al’ummar Musulmi bala’o’i illa wancan karkacewa daga kan tafarki madaidaci da gaskiya, har addini ya yi rauni tare da shuɗewar kwanaki, ƙarfinsu ya zagwanye suka kai cikin halin da suke a yau. Addini ya zama bako Musulmi kuma ko kuma waɗanda suke kiran kansu Musulmi suka zamanto ba su dawani Majiɓinci bacin Allah kuma ba su da wani mataimaki gare su hatta a kan mafi rauni daga makiyansu da mafi kaskanci masu yi musu hawan ƙawara.
Lalle Imamai (A.S.) sun yi jihadi wajen nesantar da duk wanda ke da alaƙa da su daga taimakekeniya da azzalumai, sun kuma tsanantawa mabiyansu game da tafiya tare da ma’abuta zalunci da ja’irci da cuɗanya da su. Abinda aka ruwaito daga gare su game da haka a wannan babin ba zai ƙididdigu ba, daga ciki akwai abinda Imam Zainul Abidin (A.S.) Ya rubuta zuwa ga Muhammad Bin Muslim Az-Zuhri bayan ya gargaɗe shi game da taimakon Azzalumai a kan zaluncinsu?
“Ashe kiransu gare ka yayin da suka kira ba su sanya ka ɗan dutsin niƙa suna juya zaluncinsu da kai ba, da kuma bango da suke ƙetarawa ta kanka zuwa bala’insu, da tsani na bi ta kai zuwa batansu, mai kira zuwaga zaluncinsu, mai shiga tafarkinsu, suna sanya shakku da kai a zukatan malami, kuma suna jan zukatan jahilai da ki zuwa gare su, waziransu da mafiya karin mataimakansu ba su kai inda ka kai ba wajen nuna ingancin ɓarnarsu, da shigi da ficin keɓatattu da gama gari zuwa gare su, abinda suka ba ka ya karanta matuka a kan wanda suka karɓa daga gare ka, abinda suka rayar gare ka ya karanta kwarai akan wanda suka rusa maka ka duba zuciyarka, domin babu wani mai duba ta bacin kai, ka yi mata hukunci, hukunci irin na mutum abin tambaya.
Wasiƙa daga MUSTAPHA MUSA a Kaduna. 08168716583/07014606518.