AfriHub ta jagoranci bikin Ranar Mata ta Duniya a Bauchi

Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi

Kasancewar Majalisar ɗinkin Duniya ta ware kowace ranar 8 ga watan Maris a matsayin ranar mata ta duniya, ƙungiyar Afrihub mai samun tallafin ‘Plan international da Global Affairs Canada’ ta gudanar da gangamin wayar da kan jama’a don kare haƙƙin mata da inganta rayuwar su a makarantu da yadda suke zaune da iyalansu.

Dr. Sabaatu Danladi Elizabeth Daraktar ƙungiyar Afrihub a Nijeriya ita ne ta jagoranci gangamin a Bauchi.

Yadda ta ja hankalin gwamnati da Jama’a su taimaka wa mata don su ƙara inganta rayuwar su don martaba al’umma ta hanyar rainon mutane da za su taso a yi alfahari da su wajen gina ƙasa.

Sabaatu Danladi ta ƙara da cewa, rana ce ta karrama mata saboda idan hankalin mata ya kwanta a cikin gida dole hankalin mai gida da yara ya kwanta, Amma idan mata ba su da kwanciyar hankali dole hankalin gida ya tashi.

Don haka ta buƙaci mata idan zaɓe ya zo, su zaɓi mata ‘yan uwan su. Saboda haka idan mace ta samu matsayi ta martaba mata ’yan uwanta da suka zo ganin ta. Saboda wulakanta mata da ‘yan uwan su mata ke yi idan suna riƙe da matsayi shi ke haifar da idan mata sun fito siyasa mata ba sa zabar su.

Hajiya Halima Dimis shugabar ƙungiyar inganta rayuwar mata ta HILWA a Bauchi ta roƙi hukumomi su riƙa bayar da matsayi wa mata don samun muƙamai da za su bayar da gudunmawa wajen gina ƙasa da jama’arta.

Don haka ta ce a cikin majalisar dokokin Bauchi babu mace, amma a majalisar zartaswa Gwamna Bala ya sa mata, a ƙananan hukumomi ko ina akwai mata kansiloli. Don haka ta buƙaci mata su tashi su nemi na kansu don tsira da mutuncin su da na Iyalai.

Itama shugabar ƙungiyar mata ’yan jarida ta jihar Bauchi NAWOJ Hajiya Rashida Yusuf ta ja hankalin mata ‘yan jarida kan su ci gaba da wayar da kan mata game da yadda za su inganta rayuwar su ta hanyar neman abin kan su don samun inganta rayuwarsu da ta iyalan su don a samu raguwar rasa rayuka a cikin gidaje sakamakon rashin fahimta.