Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya buƙaci Nijeriya da sauran ƙasashe masu tasowa da su rage yawan bashin da suke ɗauka, yana mai cewa tarin bashi mai yawa na “hana tattalin arziki numfashi.”
Shugabar IMF, Kristalina Georgieɓa, ta bayyana haka ne a ranar Litinin yayin taron tattaunawa da ƙungiyoyin fararen hula (CSO) a taron shekara-shekara na Babban Bankin Duniya da IMF da ke gudana.
A ranar 12 ga Oktoba, Hukumar Kula da Bashi ta ƙasa (DMO) ta sanar da cewa jimillar bashin Nijeriya ya kai tiriliyan N152.39 zuwa ranar 30 ga Yuni. Daga ciki, N80.55 tiriliyan (dala biliyan 52.67) ne na cikin gida, yayin da N71.84 tiriliyan (dala biliyan 46.98) ne na waje.
Rahoton DMO ya nuna cewa sha’awar gwamnati wajen ɗaukar bashi ta ƙaru tun bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki a watan Mayu 2023 — inda jimillar bashin ƙasar ta ƙaru da kaso 348.6 cikin ƙasa da shekara biyu.
Haka kuma, biyan bashin zuwa kuɗaɗen shiga (debt serɓice-to-reɓenue ratio) ya kai 156.8% a farkon watan Mayu, idan aka kwatanta da 29.1% a 2014 — alamar cewa fiye da rabin kuɗaɗen shiga na gwamnati na tafiya ne wajen biyan bashi.
A makon da ya gabata, Shugaba Tinubu ya rubuta wa majalisar dokoki neman izinin ɗaukar sabon bashi na dala biliyan 2.3 ta hanyar Eurobond da kuma fitar da sukuk na dala miliyan 500, domin sake biyan tsohon bashi da kuma gina muhimman ayyuka.
Rahoton DMO ya kuma nuna cewa Jihar Legas ce ta fi sauran jihohi bashi na cikin gida a farkon shekarar 2025 da N874.03bn, sai Ribas N364.39bn, yayin da Jihar Jigawa ta fi aaranci da N1.06bn, sai Ondo N11.76bn.
Da take magana kan yadda tattalin arzikin duniya zai iya jurewa ƙalubale, Georgieɓa ta ce lokaci ya yi da ƙasashe za su mayar da hankali kan rage bashin da ya yi yawa.
“Dole mu mai da hankali sosai wajen rage yawan bashi, domin bashi mai yawa yana hana tattalin arziki numfashi,” inji ta.
Ta bayyana cewa duk da cewa ƙasashe masu ci gaba da ƙasashe masu tasowa suna ci gaba da ƙara yawan bashin su, ƙasashe masu ƙaramin tattalin arziki suna fuskantar ƙalubalen da ba su da damar samun sabbin lamuni.
“Ko da yake wasu ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi suna rage bashin su, hakan ne kawai saboda ba su da damar samun sabbin lamuni — amma har yanzu suna cikin mawuyacin hali wajen biyan abin da suke da shi,” inji Georgieɓa.
Shugabar IMF ta ƙara da cewa hukumar za ta mai da hankali kan manufofin da za su taimaka wajen rage bashin ƙasashe.
Nujeriya dai tana cikin aasashen da Bankin Duniya ya rarraba a matsayin “ƙananan ƙasashe masu matsakaicin tattalin arziki”
