Tare da BILKISU YUSUF ALI, PhD
08054137080, [email protected]
Gabatarwa
Sana’a tana daga cikin muhimman hanyoyin da matasa da kowa zai iya dogaro da kai ta hanyar samun abin dogaron rayuwa. Amma samun nasara a sana’a na bukatar bin wasu matakai na musamman, kiyaye ka’idoji, da sanin hanyoyin rage asara. Wannan makala za ta yi bayani dalla-dalla kan matakan samun sana’a, yadda za ka yi nasara, hanyoyin rage asara, ka’idojin sana’a, da muhimmancin sana’a.
Matakan samun sana’a:
1. Neman ilimi da horarwa
Samun ilimi a fannin da kake son sana’a shi ne mataki na farko. Za ka iya samun horo a makarantar sana’a, ko koyon sana’a kai tsaye daga masu ƙwarewa. Samun ilimin sana’a abu ne mafi muhimmanci a duk lokacin da ka duƙufa neman sana’a.
2. Samun kayan aiki
Bayan horo, abu na gaba da ya kamata mai nemna sana’a ya yi shi ne tanadin abin sana’a. Tanadi kayan aikin da za ka yi amfani da su don fara sama’a. Kayan aiki masu kyau na taimaka maka gudanar da sana’a cikin sauƙi. Kayan aikin nan jari na ciki da sauran abubuwa.
3. Samun wuri mai dacewa
Bahaushe kan ce “Wai ba samun abincin ba , wurin cin , in ji ɗan tsako” don haka ba samun sana’a da ilimin sana’ar ba da ma jarin ti inda za a kasa hajar ko inda za a fara sana’ar shi ma yana da muhimmanci tunda duk wanda ya baza hajarsa neman mai saye yake. Zaɓar wuri mai kyau da sauƙin samun kwastomomi, kamar kasuwa ko unguwar da mutane ke yawan zuwa yana da matuƙar tasiri.
4. Fara sana’a
Ga mai fara sana’a yana da kyau ya fara da ƙaramin jari ko da ƙaramin skill domin samun gogewa, sannan ka rinka faɗaɗa sana’ar a hankali.
5. Ci gaba da koyo da inganta sana’a
Wa fauƙa kulli zil ilmin alim. Ka kasance mai neman sabbin dabaru da ƙwarewa don inganta ayyukanka.
Ka kasance mai tambaya yayin da duk wani abu da ya shige maka duhu ga wanda ya fi ka sani.
Yadda za ka yi nasara a sana’a:
Kula da ingancin ayyuka
Aiki mai kyau yana jawo kwastomomi da tsawon lokaci.
Hakuri da juriya
Sana’a na bukatar lokaci kafin ta fara kawo riba mai yawa don haka, kar ka yi saurin yin ƙasa a gwiwa.
Kashe kuɗi da lura
Ka tanadi yadda za ka kashe kuɗi da kuma yadda za ka samu riba.
Tallata sana’arka
Bahaushe na cewa “mai talla shi ke da riba” Yin amfani da hanyoyi daban-daban kamar social media, tallace-tallace a unguwa ko kasuwa yana da matuƙar tasiri.
Neman shawarwari
Ka nemi shawarwari daga masu sana’a da ƙwararru domin samun ci gaba.
Hanyoyin rage asara a sana’a:
Kula da kayan aiki
Ka rika gyara kayan aiki da zarar sun fara lalacewa.
Guji amfani da kayan da ba su da inganci.
Ingantattun kayan aiki na taimakawa wajen rage asara da inganta aiki.
Gudanar da kasuwanci da tsari
Ka tsara yadda za ka gudanar da sana’ar ka domin kaucewa ɓata lokaci da asarar kuɗi.
Gaskiya da amana
Gaskiya da amana shi ne ƙashin bayan kowacce irin nasara ga ɗan kasuwa. Ka zama mai gaskiya da amana ga abokan kasuwancinka kada ka cutar da su da harshenka ko da dukiyarka ko dukiyarsu. Yi gaskiya a dukkan al’amuranka domin samun kwastomomi masu aminci.
Ladabi da haƙuri
Ka kasance mai ladabi da haƙuri da juriya da kau da kai ga duk lokacin da kake hulɗa da mutane.
Muhimmancin Sana’a:
Sana’a na taimaka wa mutum samun abin dogaro da rayuwa da kuma kuɗi.
Tana rage matsalar rashin aikin yi a cikin al’umma.
Sana’a na ba matasa damar koyon fasaha da ƙwarewa.
Tana inganta tattalin arzikin ƙasa ta hanyar bunƙasa ƙananan masana’antu.
Sana’a na kawo ci gaba mai ɗorewa ga al’umma da ƙasa baki ɗaya.
Kammalawa:
Samun sana’a mai ɗorewa da nasara na buƙatar haɗaɗɗen ƙoƙari tsakanin ilimi da haƙuri da kulawa da tsara aiki. Idan ka bi waɗannan matakai da ka’idoji, za ka iya cimma burin ka na zama mai sana’a mai nasara da dogaro da kai. Sana’a ba wai kawai aikin hannu ba ce, hanya ce ta kawo ci gaba da canji mai kyau ga rayuwar mutum da al’umma bakiɗaya.
