Ina kan bakana kan zargin cin hancin dala miliyan 150 a Nijeriya – Jami’in Binance

Daga USMAN KAROFI

Shugaban sashen yaƙi da laifukan kuɗi na kamfanin Binance, Tigran Gambaryan, ya dage kan cewa zargin cin hanci da ya yi na dala miliyan 150 gaskiya ne. Ya bayyana cewa wasu ‘yan majalisar wakilai sun nemi cin hanci daga gare shi a lokacin wata ganawa da aka yi a Abuja domin dakatar da bincike kan kamfanin. Duk da cewa gwamnati da majalisar sun musanta wannan zargi, Gambaryan ya jaddada cewa abin da ya faɗa gaskiya ne.

Dangantakar Binance da hukumomin Najeriya ta ƙara yin tsami tun daga farkon shekarar 2024, lokacin da gwamnati ta zargi kamfanin da haddasa hauhawar darajar canjin kuɗin ƙasashen waje. Bayan haka ne aka kama Gambaryan da wani babban jami’in Binance, Nadeem Anjarwalla, a lokacin da suka iso Najeriya don tattaunawa. Sai dai daga baya Anjarwalla ya tsere, yayin da Gambaryan ya ci gaba da zama a hannun hukuma har sai da gwamnatin Amurka ta shiga tsakani aka sake shi.

A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, Gambaryan ya ce zargin da ya yi na da tushe, kuma ya danganta shi da abin da ya fuskanta da kuma bayanan da aka riga aka miƙawa jami’an tsaro na Najeriya da na Amurka. Ya bayyana cewa shari’ar da aka yi masa ta shafi rayuwarsa da iyalinsa. Ya bukaci a ƙyale shi ya wuce wannan lamari domin ya sami kwanciyar hankali.

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da wannan zargi, tana mai cewa ba gaskiya ba ne, tare da bayyana cewa maimakon haka, Binance ce ta bayar da tayin biyan dala miliyan biyar domin a sassauta lamarin. Wannan rikici na ci gaba da jawo cece-kuce tsakanin hukumomin Najeriya da Binance, yayin da ɓangarorin biyu ke ƙoƙarin kare kansu.