Ina nan raye ban mutu ba – Jamila Janafty

Daga ADAMU YUSUF INDABO a Kano

Marubuciya Jamila Mamy Janafty, wacce sananniyar marubuciyar yanar gizo ce da ta wallafa littafan Hausa da dama da suka haɗa da ‘Saifuddeen’, ‘Ta Fita Zakka’, ‘Gidanmu’ da dai sauransu. Ta ƙaryata raɗe-raɗin cewar Allah Ya yi mata rasuwa a ranar Asabar da ta gabata 11 ga Marsi, 2023. Zancen da ya mamaye duniyar rubutu da marubuta cikin ƙanƙanin lokaci, kamar wutar daji. Marubuciya Janafty, cikin wani gajeren rubutu da ta fitar dai, ta bayyana cewa: ba ma ita ba ce a hoton da ake ta yaɗawa da nufin ita ce, asali ma ba ta da alaƙa da wannan hoton gabaɗaya. Ga dai tattaunawar da Wakilin Blueprint Manhaja, ADAMU YUSUF INDABO, ya yi da fitacciyar marubuciyar bayan da wasu suka kashe ta da fatar baki:

MANHAJA: An ce kin mutu har an kai ki kushewa, to yanzu ke ce ɗin ko fatalwarki ce nake magana da ita?

JAMILA: (Dariya) Ni ce nan da kaina ba fatalwa ba, saboda ina nan a raye ban mutu ba. Zuƙi ta malle ce kawai irin na masu son bayar da labari kuma ba su da abun faɗa, shi ne suke vigewa da ƙirƙirar ƙaryar cewa wai na mutu. Wanda hakan ba sabon abu ba ne kashe shahararrun mutane da baki, musamman fitattun jaruman fina-finai, da mawaqa da kuma marubuta. To ni ma kusan abun da ya faru a kaina ke nan.

To ya kika ji da ana yaɗa hotonki tare da cewar kin rasu?

Gaskiya ni ban ji komai ba, da farko, saboda ban ɗauka abun zai wuce tunanina ba. Ban zata abun zai yaɗa duniya cikin lokaci ƙanƙani ba. Sannan ƙarin abun da ya sa ban tashi hankalina ba shi ne, wannan hoton da suke yawo da shi, ba ni ba ce a cikin hoton. Asali ma ba ni da alaƙa da wannan hoton gabaɗaya.

Au hoton wacce aka liqa a sanarwar mutuwar taki ke nan ba ke ba ce?

(Murmushi) ai kai ma ka san ba ni ɗin ba ce. To na ƙara faɗa ma ni ma da bakina cewa ba ni ba ce, kuma ban san ta ba, ban san ina aka samo hoton ba. Yadda ka gan shi ni ma haka na gan shi. 

Kuma ya kika fuskanci mutane da wannan al’amari?

Ai ranar da aka fara yaɗa wannan labarin ƙanzon kuregen ban san wainar da ake toyawa ba, saboda wayata na kashe ta tun daran ranar da abun ya fara yaɗuwa. Sai da safe da misalin ƙarfe Goma na safe (10:00AM) na kunna, sai ga wayar wata ƙawata marubuciya Surayyah Dahiru Gwaram ya fara shigo min tana sanar da ni ita ma ta samu kiran wayoyi ya fi a qirga a kan ana neman tabbacin na mutu ko ina nan da raina? Gaskiya ba ma ni ba hatta ƙawayena da makusantana sun sha kiran waya da amsa tambayoyin mutane a kan ko na mutun da gaske.

To wanna mataki kika ɗauka na shelantawa duniya cewar ke fa kina raye?

Na ɗauki matakin yin ‘write-up’ gajere mai taken Janafty Na Nan Raye Ba Ta Mutu. Kuma na yi status da kaina a WhatsApp, kuma posting a dandalin abokai na facebook. Haka kuma na nemi ‘yan’uwa da abokan arziki sun taya ni ƙaryata wannan jita-jitar a shafukansu na yanar gizo. Ga kuma uwa uba wanannan tattaunawa da nake yi da jaridarku mai farin jini, da ita kaɗai ma ta isa gamsar da duniya cewa, Janafty numfashinta bai ƙare ba da saura.

Wacce rana abun ya fara yaɗuwa?

Ranar Asabar ne da yamma (11 ga Maris, 2023), saboda a ranar na samu labarin rasuwar ɗaya daga cikin membas ɗin cikin groups ɗina, sunanta Ummi Hafsah da ta yi hatsari kuma Allah Ya yi mata rasuwa. Kuma ko hotonta ba mu fitar ba. To sai na bada sanarwan rasuwan nata a madadin duka members dina. Ina ga daga wannan lokacin ne sai aka sauya labari aka fara yawo da mutuwata, sannan labarin ya ci gaba da bazuwa har yau ɗin nan mutane suna ta kira da ‘charts’ domin tabbatarwa.

To amma kin san shahararrun mutane dama an saba kashe su da baki. A ganinki me ke kawo hakan?

To, zan iya cewa ƙalubale da man na matakin nasara. Kuma daman ita nasara ba ta zuwa sai da ƙalubale. To ni dai ina nan da raina ban mutu ba . Wannan abun kuma da ya faru ba zai sauya komai ba, domin daman kowane mai rai wata rana mamaci ne. Sai dai na ce Alhamdulillah ina godiya ga Allah da kuma duka masoyana, na ga ƙauna, na gode ƙwarai. Allah ya bar zaman tare har gaban abada. Amin.