INEC ta ƙara sati biyu don ci gaba da yi wa kaɗa ƙuri’a rajista

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da ƙarin wa’adin rajistar masu kaɗa ƙuri’a (CVR) da mako biyu domin ba wa ƙarin ‘yan Nijeriya damar yin rajista gabanin babban zaɓen 2027.

A cewar hukumar, matakin ya biyo bayan buƙatun da jama’a da ƙungiyoyi suka gabatar na neman a ƙara lokaci, saboda yawan mutanen da har yanzu ba su samu damar yin rajista ba.

Hakan na nufin masu shekaru 18 da haihuwa ko sama da haka, da kuma waɗanda ke son sabuntawa ko sauya bayanansu, za su cigaba da samun damar yin rajista cikin sabon wa’adin.

INEC ta kuma ƙarfafa duk waɗanda ba su yi rajista ba da su yi amfani da wannan damar kafin wa’adin ya ƙare, tana mai jaddada cewa rajistar masu kaɗa ƙuri’a na da matuƙar muhimmanci wajen ba kowane ɗan ƙasa damar zaɓar jagororinsa, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa, ranar Juma’a.

By Babaji

Leave a Reply