INEC ta karrama Sa’idu Bappah da mutum biyar a Gombe

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC a Jihar Gombe ta karrama Shugaban Sashin Injiniyoyi na hukumar Injiniya Sa’idu Bappa Yaya da wasu ma’aikata mutum 5 bisa jajircewar su a aiki a Jihar Gombe.

INEC ta karrama ma’aikatan na ta ne bisa hazaƙar a aiki kafin zaɓe da bayan babban zaven shekarar 2023 da ya gabata.

A jawabinsa a wajen taron karramawar da ya gudana a helkwatar hukumar Kwamishinan Zaɓen na Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Umar, yaba wa ma’aikatan ya yi bisa ƙwazon da suka nuna a aikin su wanda hakan ne sanadiyyar samun nasarar zaɓen da aka gudanar na shekarar ta 2023.

Da yake miƙa musu takardar shaidar karramawar wasu daga cikin ma’aikatan kwamishinan zaɓen ya ce ma’aikatan sun taka rawar gani sosai wanda hakan ya sa hukumar ta zaƙulo su daga ɓangarori daban-daban don karramawar.

A cewarsa karramawar za ta ƙara musu hazaƙa da kuma sa wasu ma su qara mai da hankali a ayyukan su domin gaba su shiga sahun waɗanda za a karrama.

Waɗanda aka karrama ɗin sun haɗa da Shugaban Sashin Injiniyoyi da gyare-gyare Injiniya Sa’idu Bappah da Abubakar Jadda mataimakin na musamman ga Kwamishinan Hukumar Zaɓen.

Sauran sun haɗa da Shugaban Ma’aikata Ibrahim Sabo, da Saidu Umar, Akanta na hukumar sai Jami’in hulɗa da Jama’a Mohorret Bigun.

Da yake jawabin godiya a madadin waɗanda aka karrama ɗin Saidu Umar, yaba wa hukumar zaɓen ya yi bisa wannan karamci da ta yi musu.

Sa’idu Umar, ya ce yana mai bada tabbacin cewa za su ci gaba da gudanar da ayyukan su yadda ya dace saboda ko ba dan a karrama mutum ba yana da kyau ya yi aiki tsakaninsa da Allah domin don haka aka ɗauke shi.

A wata zantawa da shi Injiniya Sa’idu Bappah, ya gode wa hukumar ta INEC ƙarƙashin shugabancin kwamishinan ta Alhaji Ibrahim Umar, na yadda ya gwada misali da su waje karrama su inda ya ce hakan sara ne kan gava kuma ya zama abun koyi ga ‘yan baya.

Sannan ya kirayi sauran abokan aikinsa da cewa su ci gaba da jajircewa wajen nuna gaskiya da riƙon amana wanda yin hakan zai kai su ga gamawa lafiya ko ba a karrama su ba.