INEC ta samu buƙatun rajistar zaɓe miliyan 2.4, yayin da an yi rajistar mutum miliyan 1.9 ta yanar gizo

Ya zuwa yanzu, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta samu buƙatar yin rajista guda 2,449,648 daga ranar da ta fara aikin rajistar masu zaɓe (wato Continuous Voter Registration, CVR) wato 28 ga Yuni, a cewar wani jadawalin mako-mako na aikin wanda aka fitar a ranar Litinin a Abuja.

Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta ruwaito cewa jadawalin ya kuma nuna cewa ya zuwa yanzu, ‘yan Nijeriya 1,923,725 ne su ka kammala matakan farko na yin rajistar su ta hanyar yanar gizo a cikin wannan lokacin na mako bakwai a daidai ƙarfe 7 na safiyar ranar Litinin, 16 ga Agusta.

Bugu da ƙari, INEC ta kuma bayyana cewa ‘yan Nijeriya 315,791 ne su ka kammala rajistar su ta hanyar yanar gizo ko ta hanyar ido da ido a cibiyoyin yin rajista da ke faɗin ƙasar nan, a cikin wannan tsakani tun da aka fara aikin.

Hukumar Zaɓen ta nuna cewa buƙatun yin rajista guda 2,449,64 da ta karɓa sun haɗa da masu son yin sauyin wurin zaɓe da masu son a sauya masu katin zaɓe (PVC) da masu son a gyara masu bayanan su da ke kan katin su na zaɓe, da sauran su.

A kan batun jinsi na masu buƙatar zaɓen su 2,449,64, alƙaluman sun nuna cewa mutum 1,370,469 maza ne, yayin da 1,079,179 mata ne, sannan 28,789 naƙasassu ne.

Wajen shekarun mutum kuma, alƙaluman sun nuna cewa mutane 1,592,178 matasa ne ‘yan shekara tsakanin 18 zuwa 34, sannan mutum 585,802 masu tsaka-tsakin shekaru ne daga shekara 35 zuwa 49, yayin da mutum 238,606 waɗanda su ka manyanta ne, wato ‘yan shekara 50 zuwa 69, sannan kuma mutum 33,062 dattawa ne ‘yan shekara 70 zuwa sama.

Da aka dubi rabe-raben shekarun na mutum 315,791 da su ka kammala rajistar su, an gano cewa mutum 176,379 maza ne, yayin da mutum 139,412 mata ne; wanda daga ciki kuma mutum 3,554 mutane ne masu fama da wata naƙasa.

Haka kuma aikin rajistar ya nuna cewa masu buƙatar rajista mutum 126,936 sun soma ne daga yanar gizo, yayin da masu buƙata 188,855 su ka fara tare da kammala matakan rajistar su ido da ido a cibiyoyin rajista.

Rabe-raben rajistar ta fuskar sana’a ko aikin yi kuma ya nuna cewa mutum 19,041 masu sana’o’i ne, mutum 59,441 ‘yan kasuwa ne maza da mata, 17, 482 ma’aikatan gwamnati ne, sannan 20,682 kuma manoma ne ko masunta.

Sauran sun haɗa da matan aure 26,993, da mutum 17,347 ‘yan tireda, da 5,679 ma’aikatan gwamnati, da ɗalibai 130,961, da kuma wasu 18,165 waɗanda ba a bayyana aikin su ba.

Daga jimillar mutane 1,923,725 da su ka kammala matakan rajista ta hanyar yanar gizo, Jihar Osun ce a kan gaba da mutum 346,819, yayin da Jihar Edo ke bi mata da mutum 179,422, sai Bayelsa da mutum 160,793, da kuma Jihar Delta da mutum 117,400.

Jihohi masu ƙarancin masu yin rajista ta hanyar yanar gizo sun haɗa da Inugu da mutum 6,112, sai Borno da ke bi mata da mutum 6,328 da kuma Yobe da mutum 6,363.