Kisan Musulmi a Rukuba: Sarkin Musulmi ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Filato

Daga AMINA YUSUF ALI

Majalisar Addinin Musulunci ta Ƙasa a ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III (JNI) ta yi kira ga Gwanmatin Jihar Filato da ta nemo masu aika-aikar kisan Muslmin Rukuba, don a gurfanar da su.

A cewar majalisar, wannan al’amari ya nuna ƙololuwar rashin wayewa inda Ƙungiyar Jama’atu Nasrul Islam ta yi kira ga gwamnatin jihar filato da ta yi gaggawar bincikowa tare da hukunta waɗanda suke da hannu acikin wannan mummunan aikin na kisan musulmi a hanyar Rakuba.

A wata takardar jawabin manema labarai da ƙungiyar ta wallafa, wacce take ɗauke da sa hannun babban sakatarenta, Dakta Khalid Abubakar Aliyu. An bayyana cewa, har yanzu Al’ummar musulmi ba su daina alhini da jimamin kisan gillar da aka yi wa major janar Idris M.Alkali ba a jihar ta filato. inda aka jefa motarsa a kududdufi kuma aka jefa gawar sa a rami.

Kuma har yanzu ba a ɗauki wani mataki ba an hukunta waɗanda aka kama da hannu a cikin waccan aika-aikar ba. Ya kuma bayyana cewa rashin mai da abubuwa da muhimmanci da kuma nuna ko in kula da gwamnati take yi shi ne yake jawo tashe-tashen hankula da ake yi a faɗin ƙasar.

“Ba zai yiwu mu dauke hankalinmu a kan wannan kisan gillar da aka yi wa musulmi a Rukuba ba; Muna da kyakkyawan yaƙinin wannan harin shiryayye ne kuma tsarrarre.
Abun takaici ne ace masu mulki a hannusu su danganta wannan kisan da kuskure. Hakan yana nuna cewa gwamnati ta yadda da kisan ƙabilanci ko kuma na addinai wanda ya riga ya zama ruwan dare. Babu wani rai da ya cancanci kisa ko salwantarwa ta ko wanne hali.

“Kar fa mu manta janar Idris.M Alkali Mutumin kirki ne kuma jajirtaccen soja da ya bautawa Najeriya tsawon shekaru talatin da biyar, amma har yanzu ba a hukunta waɗanda suka kashe shi ba. Ina kuma ga mutane farar hula har mutum ashirin da biyu da aka yi wa kisan gilla.

A wata majiyar, Kakakin rundunar jami’an tsaro na Jihar Filato ya bayyana cewa mutanen za su iya haura ashirin da biyu tunda ba a lissafi da wannan suka jikkata da raunuka. Ba mu fitar da rai ba da ganin an zartar da wani hukunci tsayyaye. Da wannan ne muke kiran ƙungiyar musulmi ta Ikare dake jihar Ondo da su kwantar da hankalinsu. Kada su tayar da hankali.

JNI bata manta da yadda aka salwatarda Rayuwar musulmin Ningi jihar Bauchi ba hanyar Langtang garin Filato. Sau da dama ana kashe Musulmin jihohin Gombe, Adamawa,Yobe da Borno a bangaren Riyom. Haka A 2008 aka kashe Musulmai matafiya daga Ƙasar Chadi a yankin Riyom.

Kamar kowa musulmi ko ba musulmi ba, matafiyi zai iya biyowa hanyar Filato kafin ya isa wasu garuruwa a cikin ƙasar nan.A irin haka ne Janar Idris Alkali ya gamu da ajalinsa ba dan komai ba sai dan kasancewarsa matafiyi kuma musulmi. Wanda har yanzu ba a kai ga hukunta wanda suke irin wannan mummunan aikin ba.

Sanin kowa ne da yanzu ƙabilun jos za su tare makiyaa su kai musu hari, makiyayanmu su ɗau mataki a hannunsu, yanzu za su mai da abun fa]an addini kuma su far wa suk wani musulmi da yake yankin.

Ba zai yiwu Gwamnatin jiha da ta ƙasa su zuba ido suna ganin yadda ake kashe al’ummarsu a irin wannan yanayin ba. Dole ne gwamnati ta ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki gurin ganin ta da ƙile afkuwar irin waɗannan hare-haren.

Duba da yadda aka daɗe ana ƙoƙarin samar da zaman lafiya tsakanin al’umma a garin, JNI na taraddadi da jimamin yadda abubuwa suke aukuwa a yankin Filato da kewayenta. Wannan wani ƙullallen shiri ne da ake yinsa in aka yi la’akari da irin nasarar da suke samu wurin kashe-kashen. Kamar yadda yake faruwa a Jos kwanakin nan duk sanda rigima ta tashi akan musulmi ka]ai abun yake ƙarewa.

“Ba za mu daina alhinin kisan kiyashin da aka yi wa musulmi ba ranar Idi a filin idi na Rukuba, da musulmin da aka tarewa hanya aka kashe a watan Yulin 2018. Muna sane da yadda ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam na gida dana waje suka yi watsi da nuna halin ko in kula. Da wani ɓangare ne ba musulmi ba, da yanzu Duniya ta ɗauka, ana ta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *