
Ranar 3 ga watan Faburairun 2026 za ta zama lokacin tunawa ga al’ummomi a jihohin Kano da Jigawa saboda Ministan Albarkatun Ruwa da Muhalli Injiniya Farfesa Joseph Terlumun Utsev ya buɗe sabbin ayyuka tare da ƙaddamar da fara wasu na ci-gaban ƙasa da za su bunkasa noma da tattalin arziki da samar da kariya daga ambaliya a wasu ƙananan hukumomin Kano da Jigawa.
Mai masauƙin wannan babban bako, haziki kuma jajirtatce wato Shugaban Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are Injiniya Rabi’u Suleiman Bichi da ya kasance a kullum cikin kokarin samar da ayyukan cigaba a jihohin Kano da Jigawa da Bauchi ne ya tarbe shi.
Engr. Bichi tare da Manyan Daraktocin sa da ma’aikatan Hukumar karkashin Babban Daraktan Kudi da Gudanarwa Hon.(Dr) Musa Iliyasu Kwankwaso, suna kokari babu dare ba rana domin ganin Al’ummomin jihohin Kano da Jigawa da Bauchi sun amfana da kudirin Ajandar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Renewed Hope.
Yayin ziyarar Maigirma Ministan Albarkatun Ruwa da Muhalli Engr Utsev ya kaddamar da kuma bude ayyukan cigaban kasa kamar haka:
Ya ƙaddamar da fara aikin samar da magudanan ruwa da kawo karshen zaizayen kasa a Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa. Aikin zai kawo karshen ambaliya da zaizayen kasa. Ruwan da a yanzu ke barna za’a karkatar dashi zuwa noman rani akalla sau uku a shekara.
Haka kuma, ya buɗe babban dakin taro a hedikwatar Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are dake Kano. Za’a rika amfani da dakin taro wajen koyar da matasa da mata sabbin dabarun noman zamani.
An kuma yaye kashin farko na Matasa dari biyar da aka koyar dasu dabarun noman zamani musamman noman amfani da ruwa mai karanci (Drip Irrigation) da kowane gida lambu (Every Home a Garden) da Green House da sauran su.
Ministan ya ƙaddamar da fara aikin gina madatsar ruwa a Bela dake Ƙaramar Hukumar Bichi, jihar Kano, wadda in aka kammala za ta kawo ƙarshen barazanar ambaliya da kuma samar da wajen noman rani da ruwan sha ga Al’ummar yankin tare da dabbobin su da kuma bunkasa harkokin noma.
Har ila yau, an ƙaddamar da gonan gwaji na amfani da ruwa mai karanci domin noma (Drip Irrigation) a garin Kaukau dake Karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano.
Injiniya Utsev bai samu damar zuwa ƙaddamar da wajen noman zamani dake feso ruwa daga injinan turo ruwa ba a Filin Gyada dake Kadawa Chiromawa Jihar Kano ba saboda ƙurewar lokaci.
Tun ranar da Rabiu Suleiman Bichi ya karbi shugabancin Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are a bara ya kasance a koda yaushe cikin samar da ayyukan cigaban kasa da sarrafa albarkatun ruwa dan samar da bunkasar noma musamman na rani da ruwan sha ga Al’ummomin jihohin Kano da Jigawa da Bauchi.
Hakika Rabiu Suleiman Bichi jakada ne na kwarai dake kokarin ganin Al’ummomin jihohin Kano da Jigawa da Bauchi sun amfana da Ajandar Shugaba Tinubu ta ‘Renewed Hope.
