
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnatin Tarayya za ta janye bai wa jihohi 20 kason ƙananan hukumomi daga watan Yuli sakamakon hukuncin cin gashin kai ga ƙananan hukumomin da kotun ƙoli ta yi a ranar Alhamis.
Antoni Janar na ƙasa, Lateef Fagbemi ya wakilci gwamnatin tarayya a yayin hukuncin kotun inda ta haramta wa gwamnati raba kason ta hannun jami’an ƙananan hukumomin da aka naɗa a madadin waɗanda aka zaɓa.
Mai Shari’a Emmanuel Agim wanda shi ya jagoranci shari’ar, ya bada umarnin kar a sake bada kuɗin ƙananan hukumomi ga gwamnatocin jihohinsu sakamakon yin amfani da ƙuɗaɗen ba bisa ƙa’ida ba da gwamnonin ke yi.
Agim, ya bayyana yadda gwamnoni ke sauya akalan kuɗaɗen wanda hakan ke haifar da koma-baya ga ƙananan hukumomin. Don haka, jihohi 20 da ba su da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi, za a dakatar da su daga karɓar kuɗaɗen har sai sun gudanar zaɓuka.
Jihohin da hukuncin ya shafa sun haɗa da; Jigawa, Rivers, Anambara, Imo, Kwara, Zamfara, Bauchi, Plateau, Abia, Enugu, Katsina, Kano, Sakkwato, Ondo, Osun, Delta, Akwa-Ibom, Delta, Cross-River da kuma Benue.
A watan Yuli, gwamnatin tarayya ta bai wa jihohi 36 har da Abuja kuɗin da adadinsu ya kai Naira biliyan 293.82 a madadin ƙananan hukumomi 774 da ke faɗin Nijeriya.
