Shugaba Ruto na Kenya ya sallami ministocinsa

Spread the love

Shugaban ƙasar Kenya, Ruto ya sallami sukkan ministocinsa.

Wannan na zuwa ne bayan shafe satuka da akai ana ta zanga zanga a ƙasar. Amma wannan sauyin bai shafi ofishin mataimakin shugaban ƙasa ba da sakataren ministocin.

Ya cigaba da cewa, za suyi gana sosai da mutane da dama domin samun shawarwari ta yadda za a kafa gwamnati mai inganci. Wadda zasu shawo kan bashin da ke damun ƙasar, samar da ayyukan yi da yaƙi da cin hanci

By ukarofi