Jakadan Sin a Nijeriya ya halarci bikin ƙaddamar da aikin horaswa

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Jakadan ƙasar Sin a Najeriya Cui Jianchun, ya halarci bikin ƙaddamar da aikin horar da ƙwararrun ma’aikata a fannin aikin sadarwa, a ranar 25 ga watan da muke ciki. Aiki ne da kamfanin Huawei na ƙasar Sin, da ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani ta Najeriya suka yi hadin gwiwar gudanarwa. Sauran manyan ƙusoshin da suka halarci bikin ƙaddamarwar sun hada da ministan sadarwa da tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani na Najeriya Isa Pantami, da wakilan wasu jami’o’i guda 8, da dai sauransu.

Cikin wani jawabin da ya gabatar wajen bikin, jakada Cui na ƙasar Sin ya ce, shugaba Xi Jinping na ƙasar Sin, ya jaddada buƙatar karfafa haɗin kan ƙasar Sin da kasashen Afirka, wajen aiwatar da wasu manyan ayyuka guda 9 na raya ƙasashen nahiyar Afirka, yayin taron ministoci karo na 8, ƙarƙarshin laimar dandalin haɗin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a bara.

Domin aiwatar da manufofin da shugaban ya gabatar ne, aka fara gudanar da aikin horaswa na wannan karo, wanda zai ba da gudunmawa ga yunkurin zurfafa hadin kan ƙasashen 2.

A nashi ɓangare, minista Pantami ya ce, kasancewarta ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, Najeriya na da makoma mai haske, inda ɓangaren tattalin arzikin ƙasar mai alaka da fasahohin zamani ke samun ci gaba cikin matuƙar sauri. Ya ce Najeriya ta gode wa ƙasar Sin bisa taimakon da ta samar mata, musamman a fannin raya fasahohin zamani.

Wannan aiki na horaswa, zai ba ɗaliban jami’o’in Najeriya su dubu 30, damar shiga kwas na musamman da kamfanin Huawei ya tsara, cikin shekaru 3 masu zuwa. Kana za a ƙara yawan jami’o’in da ake hulda da su zuwa 300, domin gudanar da wannan aiki.

Fassarawa: Bello Wang

By Editor