Tasirin azumi a jikin ɗan adam (3)

Spread the love

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa masu karatu Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka da ilmintarwa da ƙayatarwa, wanda ke kawo muku bayanai game da duniyar jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, ku san yadda jikinku ke aiki. 

Barkanmu da wannan lokaci na azumin watan Ramadan; fatan Allah ya karɓi ibadunmu, Amin. 

Kusan mako biyu kenan ina magana akan tasirin azumin a jikin ɗan adam. Da fatan dai har yanzu kuna biye da ni. A rubutun satin da ya wuce, na kawo bayani game da yadda azumi ya ke da tasiri ga ƙwaƙawlenmu. Kuma idan ba ku manta ba, na ce zan fi mayar da hankali ne akan gaɓɓai na musamman domin mu ga yadda azumi ke da tasiri a kansu. Gaɓɓan su ne: ƙwaƙwalwa, zuciya, kayan ciki, da sauransu. 

Bari in ɗan yi mana matashiya; Idan ba ku manta ba, na ce azumi na da muhimmanci ga ƙwaƙwalwa musamman ta yadda ya ke: ƙarfafa hanyoyin sadarwa tsakanin ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa; daƙile saurin saukowar tsufa; ƙara wa ƙwaƙwalwa ƙarfin wartsakewa; da kuma taimaka mata wajen saurin zartar da hukunci; sannan da kuma kare ta daga damuwa da cututtuka da suka keɓanta da ita ƙwaƙwalwar. Wannan shi ne bayanin rubutun wancan satin a taƙaice kenan. 

Yanzu da yardar Mai kowa, zan cigaba. Abubuwan da ban faɗaɗa bayani akansu ba game da  tasirin azumi ga ƙwaƙwalwar ɗan adam a wancan satin ba za su wuce abubuwa guda biyu ba: Na farko shi ne yadda yadda azumi ke daƙile saukowar tsufa da wuri. Manazarta daban-daban a ƙasashe sun wallafa sakamakon bincikensu game da alaƙar azumi da kuma wanzuwar ƙuruciya na tsawon lokaci. Abin da na fahimta shi ne: sun yadda cewa azumi yana hana faruwar tsufa da wuri, amma ta yaya hakan ke faruwa shi ne ba su fahimta sosai ba. Wannan ke nuna cewa akwai buƙatar zurfafa bincike a wannan fanni. 

Na biyu shi ne yadda azumi ke hana sakwarkwacewar kai, ma’ana yadda za ka ga wasu mutanen kansu kamar ya kwance, ko in ce su kan koma kamar sun zare. To azumi ya na hana wannan. Ta yadda aka gano hakan shi ne ta hanyar nazari da gwaje-gwajen kimiyya akan ƙananan dabbobi irinsu ɓeran masar da zomo. Binciken ya nuna cewa azumi na ƙara dattakun ƙwaƙwalwa da kuma inganta hankali.

To yanzu ba ra mu ga tasirin azumi ga zuciyar ɗan adam da hanyoyin jini da ke ɗamfare da ita. Fitaccen asibitin nan na ƙasar Amurka wato Mayoclinic, ya fitar da bayanin binciken da wasu manazarta su ka gudanar. Ga abinda su ka ce:” jeranta azumi ya na rage man kwalasturol marar kyau wanda ke da matuƙar illa ga hanyoyin jini a jikin ɗan adam.

Haka kuma akwai ƙwaƙƙwaran zaton azumi ya na inganta yadda jikin ɗan adam ke amfani da sukarin da ke jini. Hakan zai iya ragewa mutum haɗarin yawan ƙiba da kuma bayyanar ciwon suga, waɗannan abubuwa guda biyu duk su na jefa ɗan adam cikin haɗarin kamuwa da cutukan zuciya.”

Su ma wasu masu bincike akan lafiyar zuciya da ke wata jami’a a ƙasar Austria; Dr. Mahmoud Abdellatif da abokin aikinsa Dr. Simon Sedej, sun ce tabbas bincikensu ya nuna cewa jeranta azumi na da tasiri ga zuciya da hanyoyin jini, ta inda azumin ya ke rage kwalasturol ɗin da zai iya kwantawa ya toshe hanyoyin jini. Kuma sun yarda cewa azumin kan iya rage ingizon da zuciya ke yiwa jini domin ya zagaya kaf jiki, Wanda hakan kan rage tasirin hauhawar jini a jikin ɗan Adam.

Yanayin harbawar zuciya zai ragu, a maimakon da sauri, sai ya ɗan yi nawa, ba tare da kuma zuciyar ta gaza ba. Hakan zai bawa zuciyarka ko zuciyarki damar hutawa sosai kafin ta harba jini, sannan hakan zai rage wahalar aikin da ɗawainiyar da ta ke yi a kowanne lokaci. Hakan zai bayu izuwa ƙarin samun lafiya ga zuciyar mai azumi. 

Azumin ya na rage yawan kitse da teɓa; Wanda duk mun sani cewa su na cutar da jikin ɗan sosai. Teva tana ƙara girman kwiɓin ɗan Adam. Kuma masana lafiya su na amfani da awo na girman kwiɓin ko kugun mutum wajen yin waɗansu lissafe-lissafe na lafiya. Mutum mai girman kwiɓi ko me teɓa ya na cikin haxari iri iri, ciki har da haɗarin kamuwa da cutukan da ke addabar zuciya. Idan mutum ya na azumi, mun san cewa a na ramewa; a sanadiyyar haka, girman teɓa da kwiɓin mutum su ma su na raguwa. Iya raguwarsu, iya ƙaruwar lafiyar zuciya da ma jiki baki ɗaya. 

A wata mujalla mai taken Mujallar Azumi da Lafiya da ke ƙasar Dubai, Wanda masana da dama su ka wallafa sakamakon bincikensu a cikinsa, an faɗa cewa:” azumi ya na rage hauhawar jini. Ɗaya daga cikin hanyoyin da likitoci ke bi dan rage hauhawaar jini a jikin ɗan ita ce bayar da magani wanda zai iya rage ruwan da ke cikin jini. Idan mutum ya na azumi, ruwan da ke cikin jininsa zai shiga ƙwayoyin halittar jikinsa, daga nan sai ya fita ta hanyar fitsari. Sauran hanyoyin su ne magana, numfashi da sauransu. To kunga ashe mutum na rasa ruwan jiki yayin da ya ke azumi, wanda hakan ke da matuƙar tasiri wajen rage hauhawaar jini. Da fatan an gamsu.

Yin azumi ya na ragewa zuciya nauyin aikin harba jini mai yawa duka sassan jiki. Kar ku manta an ce idan ɗan Adam ya na azumi ruwan da ke jikinsa ya na raguwa (ta hanyar fitsari, gumi, numfashi, da magana). Ba a maye gurbin wannan ruwa da a ka rasa har sai mutum ya yi buɗe-baki. To a lokacin da muke tsaka da azumin, duba da cewa ruwan da ke cikin jini ya ragu, aikin da zuciya za ta yi na harba wannan jini izuwa sassa na jiki shima zai ragu. Wannan wata dama ce da zuciyar ɗan Adam za ta iya samu domin ƙara hutawa. 

Kawo ya zuwa yanzu dai, mun ga yadda azumi ke tasiri ga ƙwaƙwalwar ɗan adam; sannan kuma mun ga yadda azumin ke tasirin ga zuciyar ɗan adam tare da hanyoyin jinin da suka watsu ko ina a jiki waɗanda idan da za bibiye su, su na tiƙewa ne izuwa zuciya. Saboda  haka a rubutu na gaba, da yardar Sarkin halitta zan ɗauki wata gaɓar nayi bayanin tasirin azumi akanta.

Kafin nan na ke cewa ,‘yan uwa, ku tara a mako mai zuwa da Yardar Sarkin halitta, domin ci gaba da kawo muku bayani akan jikin ɗan adam. Bissalam. Ayi ibada lafiya.

By Editor