Ana ƙara samar da guraben aikin yi yadda ya kamata a rubu’in farko na bana

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Bisa ƙididdigar da hukumar ƙwadago ta al’ummar Sin ta samar, mazaunen birane da garuruwa na samun guraben aikin yi yadda ya kamata a rubu’in farkon bana, ƙarƙashin nagartattun manufofi na samar da guraben aikin yi, ciki hadda kara ƙarfin ba da horaswa, da nuna goyon baya ga sana’ar ƙirƙire-ƙirƙire, da ƙara ba da hidimma a wannan fanni da sauransu, inda yawan ƙarin mutanen da suka samun guraben aikin yi ya kai fiye da miliyan 2.85, wanda ya kai kashi 26% na adadin burin da aka tsara.

Hukumar ta nuna cewa, za a ci gaba da ingiza manufofi don tabbatar da samar da guraben aikin yi, ciki har da rage buga haraji da kuɗin inshorar al’umma, da goyon bayan bunƙasuwar ƙanana da matsakaitan kamfanoni, da ba da kulawa ga sana’o’i da suka fi fama da illar cutar COVID-19, da tsai da manufofin taimakawa matasa masu kammala karatu daga makarantu wajen samun guraben aikin yi, da daidaita matsalolin da ɗalibai, masu kammala karatu da manoma, da mutanen da suke fita daga ƙangin talauci, da wadanda suke rasa aikin yi da dai sauransu, da mutanen da suke da wuyar samun guraben aikin yi.

Ban da wannan kuma, hukumar za ta ƙara ƙarfin ba da horo, da hidimmomi don tabbatar da manufofin tabbatar da samun guraben aikin yi.

Fassarawa: Amina Xu

By Editor