Daga CMG HAUSA
Hukumar kula da kuɗin musanya ta ƙasar Sin, ta gabatar da wasu alkaluma a jiya Laraba, wadanda suka nuna cewa, an samu wani yanayi na daidaituwa tsakanin kuɗin musanya da kasar Sin ta samu, da wanda ta biya, cikin rubu’i na farko na bana.
An ce cikin wannan wa’adi, yawan kuɗin musanya da aka zuba wa kasuwannin ƙasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 107, adadin da ya zama mafi yawa a tarihi.
Wasu masana ilimin tattalin arziki sun nuna cewa, yayin da ƙasar Sin ke ci gaba da aiwatar da matakai don tabbatar da ƙaruwar tattalin arziki cikin gida, za a fara ganin alamar gudanar tattalin arzikin ƙasar cikin wani nagartaccen yanayi, kana kuɗin musanya da ƙasar za ta samu, da wanda ta biya, za su ci gaba da zama cikin daidaito.
Fassarawa: Bello Wang
