Jakadan Sin a Nijeriya ya halarci dandalin Abuja na 2022

Daga CMG HAUSA

Jakadan ƙasar Sin a Tarayyar Najeriya Cui Jianchun, ya bayyana cewa, hulɗar da ke tsakanin Sin da Najeriya na ta bunƙasa a shekarun baya-bayan nan, kuma sassan 2 na ƙara inganta amincewar juna ta fuskar siyasa, kana haɗin gwiwarsu ta fuskar tattalin arziki, ya haifarwa jama’ar su alherai.

Baya ga haka kuma, ƙasashen 2 sun riƙa kyautata taimakawa juna ta fuskar tsaro tsakanin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, tare da yin mu’amalar al’adu a tsakaninsu.

Ya ce ƙasar Sin na son ci gaba da aiwatar da manyan tsare-tsaren ci gaba da bunƙasa na 5GIST tsakaninta da Najeriya, bisa ra’ayi ɗaya da shugabannin ƙasashen 2 suka cimma.

Cui Jianchun ya fadi haka ne a yayin da yake halartar taron dandalin tattaunawar Abuja ta shekarar 2022 ta kafar bidiyo a ranar 13 ga wata.

Mahalarta taron sun yaba da hulɗar da ke tsakanin Sin da ƙasashen Afirka, sun kuma amince da manyan nasarorin bunƙasuwa da kasar Sin ta cimma, ƙarƙashin shugabancin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin.

A ganinsu, shawarwarin da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gabatar dangane da bunƙasar duniya da tsaron duniya, da kuma yadda ya jaddada ruhin haɗin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, a yayin taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, sun ba da jagoranci kan haɗin kai a tsakanin sassan 2 a mataki na gaba.

An kafa dandalin tattaunawar Abuja a shekarar 2018, wanda kwalejin nazarin Afirka ta jami’ar horar da malamai ta Zhejiang, da cibiyar nazari ta Gusau ta Najeriya suke gudanarwa cikin hadin gwiwa a duk bayan shekaru 2.

A bana, an gudanar da taron karo na 3, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen yin mu’amala a tsakanin kwararru na Sin da Afirka.

Wasu tsoffin jami’an gwamnatoci da ƙwararru daga Sin, da Najeriya, da Kenya, da ‘yan kasuwa, da ‘yan jarida sun tuntuɓi juna, da yin mu’amala a fannonin zaman lafiya, da tsaro, da rage talauci, da kawo wa manoma alheri, da sa kaimi kan yin ciniki, da yin ƙirƙire-ƙirƙire da fasahar zamani da dai sauran.

Mai fassara: Tasallah Yuan