ASUU ta umarci malamai su koma bakin aiki ba tare da ɓata lokaci ba

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta janye yajin aikin da take yi a hukumance tare da bai wa mambobinta umarnin su koma bakin aiki ba tare da wani jinkiri ba.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da shugaban ASUU na ƙasa, Emmanuel Osodeke ya fitar a ranar Alhamis bayan kammala taronsu a Abuja.

Shugabannin ƙungiyar sun gudanar sa taron nasu ne domin sanin mataki na gaba da ya kamata su ɗauka biyo bayan umarnin da kotu ta ba su a makon jiya na su koma bakin aiki.

ASUU ta shafe wata takwas tun bayan da ta soma yakin aikin nata inda sai a wannan karon ta janye yajin aikin nata ba tare da cimma buƙatunta ɗari bisa ɗari ba.

Ƙungiyar ta ɗauki matakin shiga yajin aikin ne domin neman haƙƙoƙin mambobinta da ta ce sun maƙale a wajen gwamnati.