Buhari ya ba da umarnin buɗe kamfanin simintin Ɗangote da ke Obajana

Daga BASHIR ISAH

Shugaba Buhari ya ba da umarnin a gaggauta buɗe masana’antar simintin nan ta Ɗangote da ke Obajana, Jihar Kogi.

Gwamnati ta ba da umarnin haka ne a taron Majalisar Tsaro da ya gudana a Fadar Shugaban Ƙasa ƙarƙarƙashin jagorancin Shugaba Buhari ranar Juma’a.

Bayanin sake buɗe masana’antar ya fito ne daga bakin Ministan Harkokin ’Yan sanda, Mohammed Dingyadi da takwaransa na Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola da kuma Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor yayin da suke yi wa manema labarai jawabi jim kaɗan bayan taron.

Aregbesola ya ce, an cimma yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Jihar Kogi da Kamfanin Ɗangote kan buƙatar a buɗe kamfanin, tare da kira ga ɓangarorin da lamarin ya shafa da su mutunta yarjejeniyar.

Kazalika, Ministan ya ce, Majalisar Tsaron ta bayar da umarnin buɗe kamfanin simintin tare da cewa, duk wata matsala tsakanin masu taƙaddama a warware ta ta hanyar shari’a. Yana mai cewa, burin gwamati ne samar da aikin yi ga ‘yan ƙasa.

Kafin wannan lokaci, Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayar da umarnin rufe kamfanin na Ɗangote a bisa wata taƙaddama da ta taso a tsakanin gwmanatin jihar da kamfanin kan mallakar masana’anatar simintin.