Sojoji sun kama tabar wiwi ta Naira miliyan 4.9 a Yobe

Daga MOHAMMED AL-AMEEN a Damaturu

Rundunar sojoji ta haɗin gwiwa ta shiyyar Arewa maso Gabas da ke Damaturu a Jihar Yobe ta miƙa buhunan tabar wiwi guda 98 wanda kuɗinsu ya kai Naira miliyan 4.9 ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA).

Kwamandan sashin, Manjo-Janar Koko Isoni ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke miƙa wa hukumar kayayyakin da aka kama a ranar Litinin a Damaturu.

Kwamandan, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Birgediya Janar Umar Mu’azu, ya ce dakarun bataliya ta 159 da ke Ƙaramar Hukumar Geidam ne su ka kama kayan a ranar 7 ga watan Oktoban 2022.

“Mai dakon kayan ya watsar da su, ciki har da motar da ke ɗauke da kayan lokacin da ya ga tawagar sintiri,” inji shi.

A nasa jawabin, kwamandan NDLEA na jihar, Aliyu Yahaya, ya yaba wa rundunar sojin bisa wannan ƙwazo, inda ya ƙara da cewa kowanne ƙunshi na tabar ya kai Naira 50,000.

Yahaya wanda ya samu wakilcin mataimakin kwamandan jihar, Ogar Peter, ya yaba da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro a jihar.

“Mun yi farin cikin samun wannan nasara. Wannan karimcin ya nuna haɗin kai da ke tsakanin jami’an tsaro a jihar,” inji shi.

Ya ƙara da cewa rundunar sojin Nijeriya ta duƙufa wajen daƙile safarar miyagun ƙwayoyi a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *