Jami’ai sun kai sumame wuraren da ake aikata laifukan ‘One Chance’ a Abuja

A ranar Laraba da yamma, rundunar kwamitin tsaron babban birnin tarayya (FCT) ta gudanar da sumame kan wuraren da ake zargin masu aikata laifin ‘one chance’ ke ɓoyewa, tare da kama wasu motoci. Sumamen ya gudana a wurare kamar Area 1, gadar Apo zuwa shataletalen na Apo, shataletalen Berger da Banex Junction.

Wannan aiki yana daga cikin shirye-shiryen hukumar don rage aikata laifuka yayin kakar bukukuwa a Abuja. Daraktan sashen ayyukan tsaro na FCT, Adamu Gwary, ya bayyana cewa manufar aikin ita ce tabbatar da tsaron birnin yayin bukukuwa da bayan su. Gwary, wanda ya samu wakilcin Dakta Peter Olumuji, sakataren cibiyar umarni da iko, ya ce za a ci gaba da aikin har zuwa watan Janairun shekara mai zuwa.

A cewarsa, an fara aikin tun farkon mako, kuma an kama wasu bara-gurbi da ake zargin suna da hannu a aikata laifuka. “Mun fara wannan aiki a ranar Litinin, kuma za mu ci gaba har bayan bukukuwa domin hana ɓarayin damar aikata miyagun ayyukansu,” in ji Olumuji.

Ya kuma bayyana cewa aikin yana da nufin magance matsalar masu aikata ‘one chance,’ daƙile haramtattun tashoshin mota da kuma kawar da bara a cikin birnin. “Matsalar ‘one chance’ tana ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen tsaro a FCT. Wannan aiki yana goyon bayan ƙoƙarin da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro suke yi don kawar da ɓarayin da suke fakewa da sana’ar tuƙin mota,” ya ƙara da cewa.

Haka zalika, daraktan ya tabbatar da cewa an kama mutane da dama yayin sumamen da aka gudanar ranar Laraba. Ya ce aikin zai ci gaba domin tabbatar da cewa birnin Abuja ya kasance cikin tsaro da kwanciyar hankali yayin wannan lokaci na bukukuwa.