Matatar Kaduna za ta dawo aiki a Disamba – Darakta

Daga BELLO A. BABAJI

Darakta-Manaja na Kamfanin tace Man fetur na Kaduna (KRPC), Dakta Mustapha Sugungun ya sanar da cewa za a kammala aikin gyaran matatar Kaduna zuwa ƙarshen 2024.

A baya ne Kamfanin Man fetur na Ƙasa (NNPCL) ya bada kwangilar gyaran matatar ga kamfanin ‘Daewoo Engineering and Construction’ na ƙasar Koriya ta Kudu akan kuɗi Dala miliyan 741.

Kammala aikin zai taimaka wajen samar da ganga 110,000 a kullum daga matatar wanda hakan zai ke wakilci kaso 60 zuwa na nan da watan Disamba, 2024.

Mista Sugungun ya ce da zarar an kammala aikin, za a samu damar ɗaukar ayyuka da kuma bunƙasar harkokin kasuwanci acikin al’umma.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su bada haɗin-kai wajen ganin an kammala aikin don amfanin ƙasa baki ɗaya.