Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Jami’an tsaro sun harbe mutane huɗu tare da raunata wasu 16 a yayin atisayen rushe gine-gine da gwamnatin Jihar Kano ta gudanar a Rimin Zakara, kusa da Jami’ar Bayero ta Kano, a Ƙaramar hukumar Ungogo.
Rusau din, wanda ya shafi gine-gine sama da 18, ya faru ne a daren Lahadi, lamarin da ya haifar da turjiya daga mazauna yankin, waɗanda suka ce ba a basu isasshiyar sanarwa ba kafin rushewar.
Wani ganau, Malam Sunusi Ɗan-Baba, ya shaidawa SolaceBase cewa tawagar rusau ta iso da daddare, inda suka fara ruguza gidaje da shaguna. ya bayyana cewa ana taƙaddama kan mallakar filin tsakanin Jami’ar Bayero da mazauna yankin tun sama da shekaru 20 da suka gabata.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) reshen Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa an tura jami’an tsaro don kare kadarorin gwamnati, amma mazauna yankin sun kai musu farmaki, sun raunata jami’i ɗaya, tare da lalata motocin su.
A nata ɓangaren, ma’aikatar filaye da tsare-tsare ta Kano ta tabbatar da cewa filin na Jami’ar Bayero ne, kuma an bi duk hanyoyin doka kafin rusau din.
Daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar, Umar Abdu Kurmawa, ya ce an bayar da sanarwa tun kafin aiwatar da rusau din, har ma an biya diyya gawaɗanda abin ya shafa sama da shekaru 20 da suka wuce.
Ya zuwa yanzu dai lamarin ya haifar da cece-ku-ce a tsakanin mazauna yankin, inda suke buƙatar a gudanar da bincike kan kisan mutanen da aka yi, tare da fayyace mallakar filin da ake taƙaddama a kai.
Blueprint Manhaja ta yi ƙoƙarin jin ta bakin daraktan hulɗa da jama’a na Jami’ar Bayero, Malam Lamara Garba, hakan bai yi nasara ba, domin wayarsa taƙi tafiya.
