Jami’an tsaron gaɓar tekun Amurka sun jinjina wa Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jami’an tsaron gaɓar tekun Amurka sun yaba wa Nijeriya, da hukumar Kula da Harkokin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NIMASA), bisa abin da hukumar tsaron gaɓar ruwan ta bayyana a matsayin “gagarumin ci gaba wajen aiwatar da dokar tsaron jiragen ruwa da tashoshin jiragen ruwa ta ƙasa da ƙasa (ISPS)”.

Joe Prince Larson na jami’an tsaron gaɓar tekun Amurka ne ya bayyana hakan wanda ya jagoranci wata tawaga daga shirin tsaro na tashar jiragen ruwa ta ƙasa da ƙasa a rangaɗin aiki a wasu tashoshin jiragen ruwa a Nijeriya domin tabbatar da matakin aiwatar da dokar ta ISPS a duk faɗin Nijeriya.

Tun da farko dai tawagar ta gudanar da ziyarar tantance ma’aikatan tashar ruwa ta Dangote da Lekki da ke jihar Legas, da kuma wasu tashoshin jiragen ruwa masu zaman kansu da kamfanin Matriɗ da Julius Berger ke gudanarwa a garin Warri na jihar Delta.

Shugaban sashen hulɗa da jama’a, Osagie Edward, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin ya ce, yayin da ya ke gabatar da rahoton tantancewar wucin gadi ga Hukumar NIMASA, Larson ya bayyana cewa yadda Nijeriya ke bin ƙa’idojin ISPS na daga cikin mafi kyawu a duniya.

Ya ƙara da cewa, tawagarsa za ta kai rahoton sakamakon binciken nasu ga shugabannin hukumar tsaron gaɓar tekun Amurka, ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa NIMASA na da ƙarfin kiyaye manyan ƙa’idojin da aka cimma a yau.

By ukarofi