Jami’ar Jihar Sokoto ta kori manyan ma’aikata uku saboda cin zarafin mata da wasu laifuka

Spread the love

Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto (UDUS) ta kori wasu manyan ma’aikata guda uku saboda karya dokokin makarantar, wanda suka haɗa da canza sakamako, cin zarafi ta hanyar lalata, da rashin halartar aiki.

Kakakin jami’ar, Ismail Yauri, ya bayyana cewa an amince da korar ma’aikatan ne a yayin taron majalisar gudanarwa ta 171 da aka yi a ranar 12 ga Maris, 2025.

Yauri ya ce wannan hukunci ya yi daidai da manufofin jami’ar na “ yaƙi da rashin ɗa’a,” wanda ke nuna tsauraran matakai kan duk wasu halayen da suka saɓa doka.

Ya ƙara da cewa: “An riga an aika wa waɗanda abin ya shafa da takardar sanarwar korar su. Wannan mataki yana nuni da jajircewar jami’ar wajen tabbatar da adalci da kuma samar da ingantaccen yanayi ga ma’aikata da ɗalibai.”

Jami’ar ta jaddada cewa wannan mataki yana da muhimmanci wajen tabbatar da nagarta da mutunta ƙa’idojin gudanar da aiki da kuma kare martabar ilimi.

By ukarofi