Idan kuɗinka na ɓatan dabo bayan dawo wa gida, saka kwararon roba don kama ɓarawon – Jarumi RMD

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Daya daga cikin ababen da ke ci wa maza tuwo a ƙwarya musamman ma na wasu ƙabilun ba hausawa ba, akwai layar zana da kuɗaɗensu ke yi bayan sun dawo gida, wanda suke da tabacin sun bar su a ciki, saidai zuwa safe sai su neme su su rasa. Abin al’ajabin kuwa shi ne, duk iya ƙoƙarinsu na gane wanda ya ɗauke su, abin zai ci tura, domin matansu ne mafi kusanci da lalitar, kuma a kullum amsarsu iri ɗaya ce, wato ba su san yadda aka yi ba, kuma ba su san wanda ya ɗauki kuɗin ba.

A ‘yan kwanakin baya ne, a wani biki, MC ɗin ya gabatar da wata wasa da za a yi, wadda ya soma kan mazan, inda ya ce, duk namijin da ya san kuɗi daga lalitarshi sun taɓa samun ƙafafu sun gudu a lokacin da ya dawo gida, to ya ta shi ya yi rawa. Ai kuwa kusan duk namijin da ke wurin taron sai da ya miƙe.

Da aka dawo wurin mata, mai gabatarwar ya umurci duk wata mace da ta san ba ta taɓa zaro kuɗi daga walet ɗin mijinta ba, ta miƙe ta taka rawa, a nan ne mata da ba su fi uku ba suƙa miƙe.

Wannan ta kasance wata ɗabi’a da ta zama ruwan dare a tsakanin matan da ba Hausawa ba, duk da cewa har a hausawan akan samu, saidai ba su yi yawa sosai ba, domin a ana mu ɓangaren yin hakan yana da illa sosai, kuma ana ƙyamatar mai yin. Saɓanin wasu ɓangarori, abu ne marar kyau, saidai bai kai munin yadda muke kallonsa ba.

Da wannan ne fitaccen jarumi a masana’antar Kudu, wato Nollywood, RMD, jarumin shahararren fim ɗin nan da ya sha suka kuma ya samu karɓuwa a lokaci guda, sakamakon salon turawa na bayyana tsiraici da fim ɗin ya ɗauka, wato ‘Shanty Town’, ya bayyana wa maza ma’aurata maganin ɓatan kuɗinsu yayin da suka zo gida, inda yake cewa, “Zuwa gare ku mazan aure, idan ku ka fahimci kuɗinku na yin ɓatan dabo daga lalitarku a duk lokacin da ku ka dawo gidanku, abinda ku ke buƙatar aikatawa don shawo kan matsalar shi ne, ku nemi kwararon roba, da kuma shedar samun ciki daga likita mai ɗauke da sunan wata, idan kun yi hakan, ku je falonku, ku zauna cikin kwanciyar hankali, kuma kwankwaɗar lemu mai sanyi, ba tare da wata wahala ba, ɓarawon zai bayyanar da kanta, wannan alƙawari ne na yi maku.”

By ukarofi