Furodusa Abubakar Galadima ya zama jakadan Zahir Spice Curry

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU

Daya daga cikin fitattun furodusoshi a masana’antar finafinai ta Kannywood, Abubakar Galadima shi ma a wannan shekarar likkafar sa ta ci gaba inda ya samu matsayin Jakadan garin sinadarin girki na ZAHIR SPICE CURRY POWDER wanda zai shafe tsawon shekaru biyu a matsayin jakadan.

Abubakar Galadima dai fitaccen furodusa ne da aka daɗe ana damawa da shi a masana’antar finafinai ta Kannywood tsawon shekaru da dama, a matsayin sa na furodusa. 

Domin kuwa tun a shekarar 2001 kamfanin sa na A S G MOVIES yake shirya finafinai, wanda zuwa yanzu ya shirya finafinai masu yawa da suka hada da; ‘Alkawari’, ‘Badini’, ‘Juyin Zamani’, ‘Hakkin Uwa’, ‘Bazata’, ‘Ya kamata’, ‘Kurman gari’, ‘Sajida’, ‘Sarina’, da sauransu. 

Haka nan a ɓangaren tallace-tallace ya yi wa kamfanoni da dama talla waɗanda ake saka wa a cikin finafinai da kuma sauran kafafen sadarwa.

A Lokacan da muka ji ta bakinsa dangane da irin rawar da yake taka wa a masana’antar finafinai ta Kannywood Abubakar Galadima ya bayyana mana cewar,

“Ita masana’antar finafinai ta Kannywood tana da girman da duk wanda ya zo da basirar sa zai samu gurbin da zai samu rabon sa, saboda masana’anta ce da Allah ya yi mata albarka da kowanne ɓangare. Zaɓi kawai ya rage wa mutum ya zaɓi wajen da zai gwada baiwar da Allah ya ba shi domin ya samu arziki.”

Ya ƙara da cewa, “Idan ka duba ni ina matsayin furodusa ne a nan na fi ƙwarewa tun da na shigo harkar. Amma ka ga a cikin hakan na ke samun damar da har nake yi wa wasu kamfanoni tallace-tallace. Duk da cewa an fi sanin jarumai da tallace-tallace a masana’antar, amma ni sai Allah ya sa na haɗa biyun har ta kai ga a wannan shekarar na samu zama kakadan garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry Powder, wannan kuma abin alfahari ne a gare ni da ma ‘yan masana’antar finafinai ta Kannywood bakiɗaya. Don hakan ya nuna nan gaba ƙwarewar mutum za a kalla a ba shi jakadancin wani kamfani ba yawan fitowar sa a fim ba.”

Da muka tambaye shi ko ta ya ya ita masana’antar za ta ci gajiyar wannan tsarin nasa?

Sai ya ce ” Ai wannan abu ne da yake a bayyane, masana’antar finafinai ta Kannywood za ta ci moriyar ta, domin ka ga duk wani aiki da na samu ba ni kaɗai zan gudanar da shi ba, sai na jawo wasu da za mu haɗu mu yi aikin da su waɗanda su ma za su yi mini aiki na biya su. Kamar ɗaukar hoto kula da waje da wasu jarumai da za mu haɗu mu yi aikin da su. Don haka mutane za su ci abinci ta hanyar aikin da za mu yi da su, wanda hakan zai kawo ci gaba da kuma bunƙasar masana’antar. Wannan kuma wani abu ne da duk wani mai kishin harkar fim da masana’antar finafinai ta Kannywood zai yi murna da shi, don haka a matsayina na furodusa da yake son ci gaban Kannywood zan yi ƙoƙarin shiga sahun mutanen da suke jawo ci gaban Kannywood wanda shi ne babban burin mu a kullum.”

Daga ƙarshe Abubakar Galadima ya yi kira ga masu harkar fim da su yi ƙoƙarin kiyaye mutuncin su da na harkar fim domin kawo cigaba mai ɗorewa a cikin masana’antar.

By ukarofi