Jam’iyyar Labour da Peter Obi sun kasa ci gaba da gabatar da bayanai a kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar hamayya ta Labour da ɗan takararta Peter Obi sun kasa ci gaba da bayar da bahasi a ƙarar da suka shigar a gaban kotun zaɓen shugaban ƙasa, a ranar Laraba.

Kotun ta ba su ƙarfe 9 na safe a ranar Laraba, domin ci gaba da gabatar da bayanansu a gabanta ta hanyar kawo ƙarin shedu da takardu, inda aka ba su sa’a huɗu su yi hakan.

Sai dai yayin da kotun ta zauna, lauyan masu ƙarar, Awa Kalu (SAN) ya gaya wa alƙali cewa sun shirya gabatar da wasu takardu, amma kuma suka gamu da wasu matsaloli daga sakatariyarsu inda wasu ma’aikatansu biyu da za su haɗa takardun ba su da lafiya.

A kan haka ne ya nemi kotun ta ɗaga musu ƙafa zuwa ranar Alhamis (jiya).

Lauyan hukumar zaɓe Abubakar Mahmoud (SAN) da, Wole Olanipekun (SAN) na Bola Tinubu da Kashim Shettma, da kuma Lateef Fagbemi (SAN) na Jam’iyyar APC ba su qalubalanci buƙatar ba.

Sai dai lauyan INEC ɗin, wato Abubakar Mahmoud ya buƙaci kotu ta zaftare yawan kwanakin da ta ba su na gabatar da bayanansu saboda wannan matsala da suka zo da ita.

A ƙarshe dai babban alƙalin kotun, Justice Haruna Tsammani ya amince da buqatar lauyan na Labour da Peter Obi, inda ya ɗaga musu qafa har zuwa Alhamis (jiya) da ƙarfe 9 na safe.

Kotun ta ɗage zamanta zuwa ƙarfe 2 na ranar lokacin da babbar jam’iyyar hamayya ta PDP da ɗan takararta Atiku Abubakar za su ci gaba da gabatar da bayanansu.