Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya ce tilas ne Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta binciki musabbabin rashin shigar da sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa zuwa manhajar duba sakamakon zaɓen INEC (IReV).
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na ARISE, tsohon Shugaban hukumar ta INEC ya ce zai iya danganta da yawa daga cikin ƙalubalen da aka fuskanta a lokacin babban zaɓen amma ya kamata a duba batun shigar da sakamakon zaɓe.
“Kuma idan kun kasance kuna da ƙwarin gwiwa kan tsarin sai kuma a ƙarshe aka samu matsala, to ya zama wajibi ku ɗauki laifin saboda ku ne jagora,” inji Jega.
“Kuma hakan ba yana nufin ka yi ne da gangan ba saboda an yi maka sulhu, dole ne mu yi adalci wajen tantancewar da muka yi.”
Tsohon Shugaban na INEC ya ce an aiwatar da tasirin na’urar da akasin haka a tantancewar da aka yi kafin ya bar hukumar.
Ya ce “Card reader ya gaza a kashi biyar cikin ɗari na wuraren da aka tura aikin wanda kashi 95 cikin 100 na samun nasara amma ‘yan jaridu da ‘yan siyasa sun mayar da hankali ne kawai kan inda ya gaza amma ba zai tava zama cikakke ba,” in ji Jega.
“Zan iya gaya muku cewa BVAS da aka ƙera don maye gurbin na’urar tantancewa ta Card Reader yana da muhimmanci ga tsarin zaɓen, sai daia babbar gazawar da aka samu a lokacin zaɓen ya shafi shigar da sakamako ta IREV kamar yadda Shugaban ya yi alƙawari.
“Ina ganin muna buƙatar mu yi tambayoyi kan dalilin da ya sa aka kasa loda sakamakon zaɓen musamman dangane da zaɓen Shugaban Ƙasa.”
