Jerin jihohin da ba su naɗa kwamitin mafi ƙarancin albashi ba

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Kimanin jihohi 27 tare da Abuja ne ba su kai ga naɗa kwamitin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba ga ma’aikatansu.

Jihohin sune; Filato, Kebbi, Sakkwato, Nasarawa, Bayelsa, Delta, Osun, Ekiti, Zamfara, Benue, Enugu, Taraba, Gombe, Kogi, Adamawa, Neja, Anambara, Imo, Ebonyi, Oyo, Akwa-Ibom, Bauchi, Katsina, Kaduna, Cross-River da Yobe.

A wani ɓangare kuma, jihohin Kano, Kwara, Ogun, Borno, Jigawa, Ondo da Abia sun naɗa kwamitocin ƙaddamarwa. Legas da Edo ne kaɗai suka yi iƙirarin fara biyan sabon tsarin albashin.

A ranar 29 ga watan Yuli, 2024 ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan sabon mafi ƙarancin albashin bayan wani zama da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC.

Kwamishinan Labarai na jihar Legas Gbenga Omotosho, ya ce gwamnatin jihar ta na biyan sama da mafi ƙarancin albashin tun kafin a sanya shi a matsayin doka.

Jihar Edo ta ce ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ga ma’aikatanta.

Haka nan sauran jihohi na cigaba da ƙoƙarin naɗa kwamitocin fara biyan sabon albashin.

Sai dai jihohin Gombe da Kogi sun ce ba za su iya biya ba. Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ya ce ba zai iya biyan Naira 70,000 ba a yayin wani zama da jagororin zanga-zanga a ranar Talata.

Kamar haka, kwamishinan kuɗi na jihar Kogi, Ashiwaju Ashiru Idris ya ce babu ranar da aka zaɓa a matsayin lokacin fara biyan mafi ƙarancin albashi a jiharsu.

By Babaji