Jimamin ƙasa: Tinubu zai jagoranci wasu manyan ƙasa a Daura domin jana’izar Buhari a yau

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau ne Shugaba Bola Tinubu tare da wasu manyan ƙasa za su taru a garin Daura dake Jihar Katsina domin halartar jana’izar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila bisa umarnin Shugaba Tinubu ne za su rako gawar daga ƙasar Ingila zuwa gida Nijeriya.

Muryoyi daga Fadar Shugaban Ƙasa sun tabbatar wa manema labarai cewa ana sa ran gawar za ta iso Nijeriya ne a sa’o’in rana na yau ɗin.

Haka kuma ana sa ran jagororin ƙasashen Afirka ta Yamma za su halarci jana’izar tare da wasu masu alfarma.

By Babaji