Awujale na Masarautar Ijebu ya rasu bayan shafe shekaru 65 a matsayin sarki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sarkin Masarautar Ijebu, wato Awujale of Ijebuland, Oba Sikiru Kayode Adetona ya rasu.

Wata majiya da ke da kusanci da Fadar ta tabbatar wa manema labarai rasuwar Sarkin, wanda ya faru a ranar Lahadi.

Sarkin ya rasu ne sa’o’i kaɗan da sanar da rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda tsohon abokinsa ne.

A shekarar 1960, aka naɗa Oba Adetona a matsayin sarki a masarautar, wanda ya zama ɗaya daga cikin daɗaɗɗun sarakunan a yankin Yarbawa kuma masu faɗa a ji a Nijeriya.

By Babaji