Koko da ƙosai Buhari ke ci don kada a kashe kasafin miliyan N10, inji Garba Shehu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Kakakin Fadar Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ya yi ikirarin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙi amincewa da kasafin Naira miliyan 10 da aka ware don abinci ga fadar a lokacin mulkinsa.

Shehu ya faɗi haka ne a wani littafinsa mai suna ‘According to the President: Lessons from a Presidential Spokesperson’s Experience’ wanda aka ƙaddamar a Abuja makon da ya gabata.

A littafin, ya yi bayani ne akan kasancewar sa mai magana da yawun shugaban ƙasa na tsawon shekaru takwas da kuma rayuwa a fadar.

Ya ce, jim-kaɗan bayan rantsar da Buhari, jami’ai suka gabatar da ƙarin kasafin abinci na fadar, wanda a ciki akwai na Shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, masaukin baƙi da na baƙi na musamman daga waje.

Buhari ya zaɓi ya gudanar da rayuwa ne a sauƙaƙe, wanda a saboda haka ne ya ke cin irin abincin da talakawa ke ci kamar irin su koko da ƙosai, ganyen salad da wasu nau’ukan abinci da aka sarrafa su da ƙwayar hatsi da naman tinkiya da makamantansu.

Haka kuma, tsohon Kakakin ya bayyana cewa a lokacin da Buhari ya kama mulki a 2015, Babbar Sakatariyar Fadar Shugaban Ƙasa, Nebolisa Emodi ta shaida masa cewa an ware miliyan N400 domin sayen motocin alfarma ƙirar Marsandi guda biyar.

Lamarin da Buhari ya ƙi amincewa da shi, inda ya ce zai cigaba da amfani da waɗanda tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Johnathan ya bari, saboda rage kashe-kashen kuɗaɗen gwamnati da inganta hanyoyin kula da su.

By Babaji