Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta ayyana yau Litinin a matsayin hutu domin girmama marigayi Muhammadu Buhari wanda ya rasu jiya a ƙasar Landan.
Sanarwar da ta fito daga sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari, gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin babban rashi bama a Jihar Katsina har da ƙasa baki ɗaya.
“Nijeriya tayi rashin shugaba mai gaskiya da riƙon amana ga kishin ƙasa,”inji Dikko Raɗɗa.
Gwamnan ya ƙara da cewa marigayi Muhammadu Buhari ya sadaukar da rayuwar sa wajen bautawa Nijeriya.
Sai ya miƙa ta’aziyar sa ga iyalan marigayi Muhammadu Buhari da al’ummar jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya inda yayi fatan Allah kai rahama a kabarin sa.
