PDP ba za ta shiga haɗakar jam’iyu ba – Nura Ahmadi Kurfi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wannan magana ta fito ne daga bakin shugaban jam’iyar PDP reshen jihar Katsina Alhaji Nura Ahmadi Kurfi a wajen babban taron jam’iyar da ya gudana a harabar sakatariyar jam’iyar a Katsina.

Taron yazo dai-dai lokacin da itama jam’iyar ADC ta gudanar da nata taron ƙaddamar da jam’iyar a Katsina.

Ya bayyana haɗakan jam’iyu a matsayin jam’iyar da bata da shugaban ci,ba kuma jiga jigan da zasu kai ta ga nasara.

Shugaban jam’iyar sai yayi kira ga ya’yan jam’iyar da su zuwa sabuwar tafiyar da su dawo PDP domin a ceci al’umma baki ɗaya.

Jagoran adawa na PDP a jihar Katsina Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke da yake jawabi ya taya ya’yan jam’iyyar PDP murna na mutanen da suka fice daga jam’iyar da ya bayyana su a matsayin mugun iri

By ukarofi