Katsina mun yi rashin ɗan da muke alfahari da shi – Dikko Raɗɗa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan ya faɗi haka ne a lokacin da yake miƙa saƙon ta’aziyyar shi ga al’ummar Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya bisa rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Bayanin da babban jami’in hulɗa da jama’a na Gwamnan, Muhammad kaula ya fitar ya bayyana tsohon Shugaban ƙasar mai shekaru 82 a duniya, ya rasu a yau Lahadi 13 ga watan Yuli 2025 da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, a wani a asibiti a birnin Landan, bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya.

Kafin rasuwar shi ya zama shugaban ƙasar Najeriya na mulkin Soja daga Janairun 1984 zuwa Augustan 1985, daga bisani kuma ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na mulkin Dimokaraɗiyya tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana mutuwar tsohon shugaban kasar a matsayin babban rashi ga al’ummar Najeriya baki ɗaya, ya kuma yi addu’ar Allah SWT ya jikan shi da rahama.

Dujiman Katsina kuma shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majilisar wakilai Hon Aliyu Abdullahi da ƙungiyar haɗin kan Funtua da ƙungiyar yan jaridu da alummomi daban daban sunyi bayan rasuwar Muhammadu Buhari a matsayin rashi ga al’ummar Najeriya.

Sun bayyana marigayi a matsayin mutum ne mai gaskiya da riƙon amana da kawaici.

Sun ce irin wannan shugaba ƙalilan ne ake dasu a duniya wanda tun rayuwar sa bai san tara abin duniya ba,sai gaskiya da riƙon amana.

Sunyi addu’ar Allah ba iyalan sa da al’ummar Jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya haƙuri na rashi da a ka yi.

By ukarofi