HOTUNA: Yadda Shettima ya isa Landan don rako gawar Buhari zuwa Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya isa birnin Landan bisa umurnin da shugaba Tinubu ya ba shi na raka gawar tsohon shugaba, Muhammadu Buhari wanda ya rasu a jiya Lahadi zuwa Nijeriya.

Daga cikin waɗanda suka tarbi Shettima akwai gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum da Ministan Harkokin Waje, Ambasadda Yusuf Tuggar.

By Babaji