
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Dandalin Siyasa Online Forum/Dandali Foundation, a madadin baki ɗaya mambobinsu, ta bayyana kaɗuwarta game da rashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a jiya Lahadi bayan shafe shekaru 82 a Duniya.
A sanarwar da Shugabanta, Hashim Ubale Yusufu ya fitar, ƙungiyar ta ce za a riƙa tunawa da Buhari a matsayin jagora mai hangen nesa, jajirtacce kuma wanda ya bada gagarumar gudunmuwa wajen shugabancin ƙasa.
Ya ce, Buhari ya kasance ɗan dimukraɗiyyar da al’umma musamman talakawa suka amfana da tsare-tsarensa a fannin noma da al’amuransu na yau da kullum.
Ubale Yusufu ya kuma ce, rashin tsohon shugaban ƙasar, abu ne da ya shafi ba iya miliyoyin al’ummar da ke goyon bayansa ba har ma da ƙasar baki ɗaya.
Daga ƙarshe, ya yi masa addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa gami da sanya shi a Aljannar Firdausi.
