An ɗage jana’izar Buhari zuwa Talata

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya bayayna cewa sai a gobe Talata ne za a yi jana’izar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu ranar Lahadi a birnin Landan.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a fadar gwamnatinsa , Raɗɗa ya ce ya yi magana da iyalan tsohon shugaban ƙasar da kuma makusanta dake Landan dangane da shirye-shiryen ɗaukar gawar zuwa Nijeriya.

”Daga tattaunawar da na yi da iyalansa da makusantansa da ke tare da gawar, sun bayyana mana cewa ana cigaba da shirye-shiryen yadda za a ɗauko gawar zuwa Nijeriya”, inji gwamnan.

”Bayannan da na samu shi ne sai gobe da rana misalin ƙarfe 12:00 gawar za ta ƙaraso, don haka za a gudanar da jana’izar da misalin ƙarfe 2:00 na ranar gobe Talata.”

Ya ƙara da cewa za a yi jana’izar tsohon shugaban ƙasar ne a mahaifarsa da ke Daura a jihar.

By Babaji