A ranar Lahadi Jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya gamu tsaiko a hanya a yankin Jere, Kaduna, sa’a guda da fara aiki.
Jirgin mai dauke da gomman fasinjoji, ya baro Kaduna ne da misalin karfe 8:05 na safe da nufin zuwa Abuja inda ya gamu da cikas.
Bayanai sun ce kafafuwan uku daga cikin taragon jirgin ne suka sauka a layi wanda hakan ya tilasta wa jirgin tsayawa.
An ga jami’an tsaro daban-daban a wurin da lamarin ya faru don bai wa jama’a kariya.
Hukumar Binciken Tabbatar da Kariya ta Nijeriya (NSIB) ta ce ta tura jami’anta yankin domin gudanar da bincike kan lamarin.
A nata bangaren, Hukumar Jiragen Kasa ta Kasa (NRC) ta ce, duk da faruwar akasin, hakan bai hana sauran jiragen da ke jigilar fasinjoji tsakanin Kaduna zuwa Rigasa da Idu a Abuja aiki ba.
