Namiji mai duka

Daga AISHA ASAS

Idan an yi zancen namiji mai dukan matarsa a Arewacin Najeriya, ko ma ince a Ƙasar Najeriya bakiɗaya, ba a cika ɗaga kai a dube ta ba, kasancewar ta zama ruwan dare, kuma iyaye da kakani sun mata gurbi a zamantakewar aure, don haka matar da ba ta jure dukan mijinta ana sanya ta a layin marasa haƙuri.

Yayin da ka ce duka ba kyau a addinin Musulunci, to fa ka janyo wa kanka abinda za a iya kiranka ɗan tawayen addini, saboda ya yi wa masu yin sa rana.

Mazaje da dama suna kafa hujja da aya a cikin littafi mai tsarki da ta ce, “…………………ku dake su.”

Kuma idan sun ta shi kafa hujja da wannan ayar sai su tsallake farkon ta, su isa zuwa ƙarshe kamar yadda na rubuta ta.

Da wannan gurguwar fassara da suke yi wa wannan vangare Musulunci ya sha raddi ga waɗanda ba su yarda da shi ba, har suke yi wa addinin kallon addinin da ya aminta da cin zarafin mata.

Bari mu fara daga kan wannan ayar da ta yi batun duka, wadda take a cikin suratul Nisa’i, aya ta 34. Allah maɗaukakin Sarki ya ce, “Matayen da ku ke tsoron saɓawarsu, to ku yi masu wa’azi, ku ƙaurace masu a shimfiɗa, ku dake su, amma idan suka yi maku biyayya, kada ku nemi hanyar cutar da su, lallai Allah Ya kasance Mai ɗaukaka ne, Mai girma.”

Malamai sun yi bayyani kan wannan ayar akan cewa, waɗannan matakai da ayar ta zo da su, za a bisu ne ɗaya bayan ɗaya, ba tare da an tsallake wani zuwa wani ba. Ma’ana, lokacin da matarka ta zo da wani abu na sava maka ko saɓa wa Allah, to za ka fara ne da yi mata wa’azi, kuma wa’azin ba na ɗai rana ba, za a yi ana tusawa, da amfani da ‘yan dabaru na lurarwa. Za a ɗauki lokaci kana bin duk wata hanya ta yin nasiha da zai karya zuciyarta.

Idan ka yi iya yi ba ta ji ba, to sai ka isa zuwa mataki na biyu, wato ƙaurace wa shimfiɗarta, wanda akwai hikima sosai a wannan. Domin cikin ɗabi’un da mata suka fi tsana shi ne miji ya ƙaurace masu, ba wai don kawai sha’awarsu ga kwanciyar ba, sai don halin da suke da shi na tsanar ƙiyawa, wadda a ganin su, su ya dace su ƙiyawa miji ba shi ba. Kuma yin hakan gare su tamkar zubar da su ne a ƙima. Don haka da yawa mata na shiga taitayin su idan mazajensu suka guje wa shimfiɗarsu.

Idan kuwa an samu mai kafiya, ka ƙaurace wa shimfiɗarta tsayin lokaci ba ta canza ba, sannan aka ce a je ga mataki na duka. Amma kafin ka sauke numfashi zan so ka tambaye kanka, ya aka ce ka dake matarka?

Malaman tafsiri sun bayyana dukan mace a matsayin duka marar cutarwa, idan mun tattaro bayanai da suka yi za mu fahimci cewa, duk dukan da za ka yi wa matarka ta ji shi a jikinta, ko ya mata illa to bai halasta ba, daga ƙarshe ma suka tattaru akan barin dukan shi ya fi, duk da addini ya ba bada damar. Ba kuwa komai ya sa su haɗar haka ba sai don gudun wuce gona da iri kamar yadda ake yi a yanzu.

Babu ta inda addini ya halasta irin dukan da maza ke yi wa matansu a yanzu. Sau da yawa za ki tarar macen ma ba ta san laifi ta yi wa mijinta ba sai ta sanadiyyar rufe ta da duka ne za ta fahimci wani abin ta yi masa. Kuma dukan zai yi shi ne tamkar yana dambe da qato ɗan’uwansa.
Babu kallon ma ta inda yake dukan nata, bayan aya musamman ta yi gargaɗi kan kada ku dake mata a fuskokinsu.

Baya ga haka ma, ko dukan hankali za ka yi masu, to fa bai halasta ba matuƙar ba ka biyo ta waɗancan matakai da muka ambata ba.
Idan aka ɗauki mataki na farko, bayan ka yi mata nasiha na tsayin lokaci ba ta ji ba, to zai fi ka kai ƙarar ta ga wani malami da take ganin ƙimar shi, don sau da yawa mata ba su cika yarda da karatun mazajensu ba, shi ya sa wani lokacin za ka ga matan malamai na yawon zuwa makaranta ta daban ba ta mazahensu ba, don sun fi gamsuwa da abinda suka ji daga wurin wasu. Shi kuwa miji wani abin ma idan ya faɗa sai sheɗan ya sa mata san ranshi ne ya faɗa don ya tilastata ga wani abu.

Idan ta hanyar malamin ba a samu nasara ba, sai ka kai ƙarar ta ga iyaye idan tana da na ƙwarai, su ma su yi nasu faɗan da nasiha. Kun ga kuwa ko a iya nan aka tsaya, idan ba matsanancin taurin kai ne da mace ba dole za ta sauko ta dawo kan hanya.

Idan mun fahimci bayanin za mu aminta da cewa, dukan mace da ake yi ko kusa bai samu ɗaurin gindin addini ba, kuma Musulunci bai halasta shi ba, don haka kuskure ne tursasa ‘ya’yanku shanye dukan mazajensu, kuma bai halasta ku ba wa namiji mai dukan matarsa aure ba matuƙar kun sani.

Shi kuwa mai aikata wannan hukuncin sa guda da mutumin da ke zaluntar wanda ya fiya ƙarfi, sai dai shi nasa ya ɗara, domin har da cin amanar da ya ɗauka daga wurin iyayenta kafin su aura masa ita.

Daga ƙarshe zan faɗa da babbar murya, dukan da ku ke yi wa mata haramun ne! Kuma Allah zai hukunta ku akan cin zarafin da ku ke yi wa matanku, domin matayenku abokanen rayuwarku ne, kuma Mai tambaya ne akan yadda ku ka yi rayuwa da su.