Jonathan ne silar wadaƙa da kuɗin makamai a yaƙin neman zaɓe – Magu

Spread the love


Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa da Ta’annatin Tattalin Arziki (EFCC), Ibrahim Magu ya yi furucin cewar, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ne ya amince da ɓatar da zunɗurutun kuɗaɗe dala biliyƙn 2.1 da sunan yaƙin neman zaɓe.
Kamar yadda Magu ya zayyana, ma’adanin hukumar EFCC ya nuna cewa waɗannan zunɗurutun kuɗaɗe a hukumance ba a amince da su domin yaƙin neman zaɓe ba, la’akari da hujjoji dake tattare da masu bincike.
Tsohon shugaban hukumar ta EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana dalilin da ya san ya ba a yi sammacin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ba lokacin da ake yin binciken wannan badaƙalar kuɗaɗe.
Kamar yadda Magu ya zayyana, ma’adanin hukumar EFCC ya nuna cewa waɗannan zunɗurutun kuɗaɗe a hukumance ba a amince da su domin yaƙin neman zaɓe ba, la’akari da hujjoji dake tattare da masu bincike.
Wannan bankaɗe ya fito fili ne a cikin littafi mai laƙabin, ‘Daga Aikin Soji Zuwa Shugabancin Gwamnati: Abubuwan Tunawa Na Muhammadu Buhari “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari” wanda Dokta Charles Omole ya rubuta, kuma aka ƙaddamar a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.
Littafin dai ya fayyace yadda rayuwar tsohon shugaban ta kasance, lokacin da ya yi aikin soji da rawar da ya taka a fagen siyasa.
Omole ya faɗi a cikin littafin nasa cewar, ta’ammalin da kuɗaɗen makamai ya haddasa tashin-tashina a tsakanin muƙarraban jam’iyar PDP yayin da aka yi sammacin jiga-jigan jam’iyar lokacin bincike akan badaƙalar kuɗaɗen.
Marubucin littafin ya yi tuni da cewar, tirka-tirkar nuna mulki a cikin gwamnati ya sanya masu lura ke ganin tsohon mai bayar da shawara akan tsaron ƙasa, Sambo Dasuki a matsayin ‘ma’abucin’ shugaba na kwatanci da Jonathan.
“An habarto rashin jituwa a tsakanin NSA Sambo Dasuki da Ministan tsaron na wancan lokaci, Aliyu Gusau dangane da ko wane ne ke da iko ko bayar da umarnin sayo makamai dama sauran ayyuka dake da nasaba da NSA, da wasu ke ganin Dasuki a matsayin taƙwaitakar,” cewar Omole.
Littafin ya kuma ce binciken bai kammalu ba akan wasu jigogin jam’iyyar ta PDP. Tsohon shugaban jam’iyar na ƙasa, Ahmadu Mu’azu an lura da cewar ya shiga wasan ɓuya na baya-nan, baya-can, yayin da ake zargin mai magana da yawun jam’iyar, Olisa Metuh ya yi ƙememen rashin dawo da kuɗaɗen kimanin naira miliyan ɗari huɗu, da aka mirgina su zuwa wani kamfani da yake da nasaba da shi.
Zuwa watan Janairu na wancan shekarar badaƙalar, an yi sammacin tsohon shugaban jam’iyar na ƙasa Ahmadu Mu’azu domin bin ba’asi, amma ba a iske shi ba yana wasan ɓuya lokacin.
Tsohon kakakin jam’iyar ta PDP, Olisa Metuh da aka yi sammacin sa, ya bayyana cewar, ya gwammace ya daɓawa jikin sa wuƙa, da a ce ya dawo da waɗannan kuɗaɗen gararumar,” a cewar Omole.
Wasu jiga-jigai da aka ambata cikin badaƙalar sun haɗa da tsohon shugaban NIMASA, Patrick Akpobolokemi, wanda shi an cafke shi, ya kuma gujewa beli, aka sake cafko shi.
Shugabannin jam’iyar PDP na shiyyoyi shida dake ƙasar nan dukkan su suka ce sun karɓi kuɗaɗen da ba su ma san asalinsu ba.
Omole ya bayyana cewar, daga bisani Magu ya fayyace cewa ba a ma yi sammacin Jonathan ba cikin binciken, saboda babu wata takarda data nuna sa hannun amincewar sa a cikin badaƙalar kuɗaɗen da aka yi wa laƙabi na makamai ne, ko kamfen
“Shi (Magu) yaji takaicin yadda lawyoyi waɗanda akayi wa tagomashi suka yiwa sharia tarnaƙin tafiya, kututun ‘yan siyasa masu hikimar iya satar kuɗi aira biliyan goma, su keɓe kuɗi naira biliyan biyar domin fafata sharia ke hayar dakarun lauyoyi (Adɓocates) suna dagula lamuran bincike”.
Littafin na Omole ya ƙara da cewar, wasu jiga-jigan jam’iyar PDP sun zargi hukumar ta EFCC da nufin yi masu bita-da-ƙulli, yayin da fayil-fayil na ƙararraki da mayar da raddi suka yiwa dakin sharia katutu.

By ukarofi